Ban ga dalilin karrama Abiola da GCFR ba, alhalin ba ma dan Najeriya bane – Dino Melaye

Ban ga dalilin karrama Abiola da GCFR ba, alhalin ba ma dan Najeriya bane – Dino Melaye

Sanata mai wakiltar Kogi ta ya yi Allah wadai da girmama marigayi Abiola da shugaba Muhammadu Buhari yayi da lambar girmamawa ta GCFR.

Ya ce bai ga dalilin da zai sa Buhari ya mika irin wannan babbar lambar yabo ga mutumin da baya raye a duniya ba.

“Abiola ba dan Najeriya bane yanzu tunda ya riga ya rasu, ita kuma wannan lambar girmamawa a na ba rayayye ne kuma dan kasa. Haka take a doka amma ba wai don kawai ana so a burge ba sai a keta doka babu gaira babu dalili.

"Mutuwar Abiola kawai ya maida shi ba dan Najeriya ba," Inji Dino.

Ban ga dalilin karrama Abiola da GCFR ba, alhalin ba ma dan Najeriya bane – Dino Melaye
Ban ga dalilin karrama Abiola da GCFR ba, alhalin ba ma dan Najeriya bane – Dino Melaye

Dino ya ce tabbas idan har hakan zai zauna toh fa sai an yi wa dokar gyara.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya canza ranar murna da hutun dimokradiyya a kasar nan zuwa ranar 12 ga watan Yuni daga 2019.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Wata babbar kotun majistare dake Wuse, Abuja ta ba Sanata Dino Melaye (APC, Kogi) hutu domin ya tafi kasar Amurka ganin likitansa.

An gurfanar da Melaye a gaban kotu a ranar 2 ga watan Mayu kan zargin sa da yunkurin tserewa daga wani motan yan sanda a Abuja a ranar 24 ga watan Afrilu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Domin samun ingantattun labarai bide mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel