Jirgin Mataimakin shugaban kasa Osinbajo yayi saukar gaggawa

Jirgin Mataimakin shugaban kasa Osinbajo yayi saukar gaggawa

- Sauran kadan Jirgin dake dauke da Mataimakin Buhari ya fado

- Jirgin ya samu Matsala ne yayinda yayi yunkurin tashi sama

- Osinbajoon dai ya je halartar bikin kammala taron wata Makaranta ne a Abuja

Wani Jirgi mai saukar Ungulu dake da ya dauko Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo daga Makarantar Ma’aikatan Kwastam dake Gwagwalada a Abuja yayi dirar gaggawa dakiku kadan da tashinsa a yau Alhamis.

Da duminsa: Jirgin Mataimakin shugaban kasa Osinbajo yayi saukar gaggawa
Da duminsa: Jirgin Mataimakin shugaban kasa Osinbajo yayi saukar gaggawa

Mataimakin shugaban kasar dai ya kai ziyara Makarantar ne domin halartar taron kammala karatun manyan daliban kwalejin da suka yi kwas na 1/2018.

Kafin samun matsalar Jirgin, mataimakin shugaban kasar ya hau shi har zuwa Makarantar domin halartar taron.

KU KARANTA: Rashin kai zuciya nesa ya sanya wani Saurayi kashe ‘dan uwansa akan Komfuta Laptop

Amma sai dai bayan kammala taron tashinsa ke da wuya sai ya fara fitar da wani hayaki sannan ya gaza yin sama ya shallake bishiyoyin da suke wurin, hakan ta sanya tilas ya dankwafo inda ya sauka da farko kafin ya tashi.

Da duminsa: Jirgin Mataimakin shugaban kasa Osinbajo yayi saukar gaggawa
Da duminsa: Jirgin Mataimakin shugaban kasa Osinbajo yayi saukar gaggawa

Wannan matsala da Jirgin ya bayar ne ya tilastawa Mataimakin shugaban kasar tafiya ta kwallata domin komawa.

Babban hafsan Sojojin kasar nan Laftanar kanar Tukur Buratai da kuma shugaban Rundunar Sojin saman Sadique Abubakar duk sun halarci taron amma matsalar Jirgin ta faru jim kadan bayan tafiyarsu

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel