Sanatoci sun bijiro da wata sabuwar bukata kan zaben 12 Yuni

Sanatoci sun bijiro da wata sabuwar bukata kan zaben 12 Yuni

- Batun sauya ranar Dumukuradiyya na cigaba da daukar hankali

- Wasu na nuna goyon baya, amma wasu sun ce duk wani yunkuri ne na jan hankalin masu zabe a 2019

- Sai dai Majalisar Dattijai ta nuna goyon bayanta amma ta sake bijiro da wasu bukatun da ke da alaka da zaben 1993

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu yabo daga Sanatocin Najeriya bisa girmama MKO Abiola dan takarar shugabancin kasar a shekara ta 1993 tare da mataimakinsa Babagana Kingibe da yayi.

Sanatoci sun bijiro da wata sabuwar bukata kan zaben 1993
Sanatoci sun bijiro da wata sabuwar bukata kan zaben 1993

Irin wannan girmamawa abu ne wanda ya cancanta da ya kamata a ce anyi tun da dadewa a cewar shugaban majalisar Bukola Saraki.

Yayin bayyana goyon bayansu ga wannan sabon sauyi domin girmamawa da Buharin yayi, wasu Sanatocin sun kara da saura kuma Gwamnatin tarayyar ta sake mayar da ranar 12 ga watan ranar hutu a kasa baki daya.

KU KARANTA: Ranar 12 ga watan Yuni: Yadda IBB ya soke zaben shugaban kasa na MKO Abiola a shekarar 1993

Sannan kuma suka shawarci shugaban kasar da ya umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta bayyana ainihin sakamakon zaben domin ayyana Abiola a matsayin shugaban kasa tare da mataimakinsa Kingibe, sannan ya kuma sanya a basu duk wani hakki da ya cancanta a basu.

Sanatoci sun bijiro da wata sabuwar bukata kan zaben 1993
Sanatoci sun bijiro da wata sabuwar bukata kan zaben 1993

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel