Sabuwa: Yan daba sun ambaci dan majalisa a matsayin uban gidansu
Mutane hudu da ake zargi da daba sun shiga hannun hukumar yan sanda da laifin kisan wani mutum mai suna Arsenal-nice a garin Shagamu, jihar Ogun.
Yan daban masu suna - Olushola Adedeji; Olusegun Olalekan, aka Musket;Azeez aka Anene; da Abolore, aka A.B, sun shiga hannun jami’an yan sandan ne a Obada, garin Abeokuta.
Yayinda aka kaddamar da bincike, makasan sun bayyana dan majalisa mai wakiltan mazabar Sagamu 1, Yinka Mafe a matsayin mai daukan nauyinsu.
Amma kafin tayi sanyi, dan majalisan wanda shine shugaban masu rinjaye a majalisan dokokin jihar ya musanta wannan zargi.
Yace: “Ba zan yi magana kan jita-jita ba. Idan an gurfanar da su a kotu zan je a matsayin lauya in kare kaina.”
Kakakin hukumar yan sandan yankin, Dolapo Badmus, tace: “Muna gudanar da bincike. Sunce suna yiwa wani dan siyasa aiki ne amma muna muna gudanar fa bincike.”
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng