Soyayyar Uba da Da: Wani tsautsayi mai ban tausayi ya faru da wani Uba da Dansa
A wani lamari mai cike da ban tausayi da ya faru a kasar Afirka ta kudu, wani Uba ya bindige dansa har lahira a gabn Makarantarsu Yaron, inda ya jira tsawon lokaci yana jiran yaron ya tashi daga makaranta, don ya mayar da shi gida.
Gidan Talabijin na Channels ta ruwaito wannan lamari dai ya faru ne a ranar Laraba, 6 ga watan Yuni, bayan mahaifin wanda aka sakaya sunansa ya ajiye dan nasa a makaranta da yamma, inda ya tsaya jiran yaron har sai sun tashi, sai ya garzaya da shi gida.
KU KARANTA: Jirgin sama dauke da mutane 10 ya yi ɓatan dabo a sararin samaniya
Sai dai kafin yaron nasa su tashi daga makaranta, tuni bacci ya kwashe mahaifin nasa, bayan y adage gilasan widunan motar ya kunna na’urar sanyaya mota, kwatsam sai ya ji ana buga masa gilashin mota, dayake a unguwar Ennerdale ne wanda ta yi kaurin suna da miyagun mutane sai ya dauka su ne.
Don haka cikin hanzari da magagin bacci ya yi wuf ya dauko bindigarsa, ya harbata daidai inda ya ga ake buga masa kofar, kash! Ashe yaron nasa ne ya zo da nufin su tafi gida.
Kaakakin rundunar Yansandan yankin, Mpande Khoza ya bayyana cewar sai bayan da mahaifin yayi harbin ne ya sai ya fahimci ashe dansa ya bindige ba tare da laifin baki ba balle na fari, nan kuwa ya shiga cikin dimuwa yana kuwwa.
Matsalar ayyukan miyagun mutane ya yawaita a garin Johannesburg, musamman ayyukan fashi da makami, fyade, satar mota da sauransu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng