Yadda shigar banza ta jefa wasu mata 2 'yan kwalisa cikin matsala hannun jami'an 'yan sanda a Najeriya
- Wata 'yar Najeriya ta fallasa yadda jami'an 'yan sanda na SARS suka ci zarafin su
- Matar ta bayyana cewa 'yan sandan sun caje su kudi saboda sun yi shigar banza
- Matar ta bayyana cewa sai da suka biya su Naira dubu 10 sannan suka sake su
Yayin da 'yan Najeriya ke kokawa sosai game da yawaitar cin zarafin su da jami'an tsaron kasar musamman ma na rundunar SARS ke cigaba da yi a kullum, wata mata ta fallasa a kafar sadarwar zamani yadda 'yan sanda suka ci zarafin ta da kawar ta saboda wai sun yi shigar banza.
KU KARANTA: Buhari yayi nasara a kotu
A cewar matar, ta ce suna cikin tafiyar su ne sai jami'an 'yan sandan suka tsayar da motar su suka kuma umurci direban da ya yi tafiyar sa.
Legit.ng ta samu cewa matar ta kuma bayyana cewa bayan jami'an 'yan sandan sun gaba bincikar su basu same su da laifi be sai kawai suka ce ai sunyi shigar banza wadda kuma babban laifi ne.
Ta cigaba da cewa a haka dai suka cigaba da tsare su har sai da suka biyasu tarar Naira dubu 10 sannan suka kyale su.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng