Garin dadi-na-nesa: Ku kalli hotunan gidan yarin kasar Norway masu daukar hankali

Garin dadi-na-nesa: Ku kalli hotunan gidan yarin kasar Norway masu daukar hankali

Gidajen yari dai kamar yadda aka saba musamman a Nahiyar mu ta Afirika gida ne da kowa ke gudun zuwan sa musamman ma saboda irin rayuwar kazanta da kaskanci har ma a wasu lokutan hadarin gaske da ake yi a ciki.

Idanu sukan rena fata idan har alkali ya yankewa mutum hukuncin zaman gidan yari ba don komai ba sai don irin azabar da zai tarar a can tun daga abinci har zuwa makwanci da sauran abubuwan bukatun rayuwa.

Garin dadi-na-nesa: Ku kalli hotunan gidan yarin kasar Norway masu daukar hankali
Garin dadi-na-nesa: Ku kalli hotunan gidan yarin kasar Norway masu daukar hankali

KU KARANTA: Hotunan auren wata budurwa da dan shekara 90

Legit.ng ta samu cewa sai dai a wasu kasashen musamman ma na yamma ba hakan lamarin yake ba domin kuwa inda aka kebe domin masu aikata laifin kai kace ma gidajen alfarma ne na sarakunan su da wasu hamshakan masu kudi.

Garin dadi-na-nesa: Ku kalli hotunan gidan yarin kasar Norway masu daukar hankali
Garin dadi-na-nesa: Ku kalli hotunan gidan yarin kasar Norway masu daukar hankali

Kasar Norway ma dai dake zaman daya daga cikin kasashen turai tana cikin kasashen da gidajen yarin ta suke da matukar daukar hankali kamar dai yadda wani ma'abocin kafar sadarwar zamani ta Tuwita Arthur Musinguzi ya nuna.

Tabbas hotunan sun saka mutane daga sassa daban daban na Najeriya tofa albarkacin bakin su inda wasu har ma suke fatan Allah ya kai su ciki.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel