Dalilin da yasa nake saka irin kayan da nake sakawa a wakoki na – Adam Zango

Dalilin da yasa nake saka irin kayan da nake sakawa a wakoki na – Adam Zango

Shahararren jarumin nan na kannywood kuma mawaki, Adam A.Zango yayi Magana akan korafin da jama'a keyi game da irin kayan da yake sanyawa a cikin bidiyon wakokin shi.

A wata hira ta musamman wanda ya wallafa a shafin sa na zumunta, Zango ya bayyana cewa ya na sanya irin kayan zamanin ne domin janyo hankalin jama'a wajen kallon wakokin yan arewa.

Yace dabarar yin haka shine domin jawo hankalin samari da yan mata masu kallon wakoki kasar waje da na kudancin kasa zuwa kallon nashi.

Ya kara da cewa mafi yawanci mabiyan sa masu bibiyan wakokin turawa da na india basu san kalamai da mawakan ke furtawa a cikin wakokin su kuma mafi yawanci kalamai ne wanda bata dace ba wanda bahaushe kuma musulmi ya dinga furtawa.

Dalilin da yasa nake saka irin kayan da nake sakawa a wakoki na – Adam Zango
Dalilin da yasa nake saka irin kayan da nake sakawa a wakoki na – Adam Zango

A cewar sa yana kokari wajen rera wakoki cikin yaren hausa kuma ya sanya mata kida irin ta zamani kuma ya sanya kayan zamani a cikin ta domin janye hankalin jama'a zuwa kallon nashi.

KU KARANTA KUMA: Matakan tsige shugaban kasa 8 a kundin tsarin mulkin Najeriya

Ya jadadda cewa hakan yunkuri ne na janyo hankulan mutanen arewacin kasar wajen yin alfahari da mawakan yankinsu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Domin samun ingantattun labaranmu bide mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng