Sojojin Ruwa sunyi gagarumar nasarar kama shinkafa har buhu 2,860 daga wajen ‘yan fasa kwauri

Sojojin Ruwa sunyi gagarumar nasarar kama shinkafa har buhu 2,860 daga wajen ‘yan fasa kwauri

- Wasu masu fasa kwauri sun gamu da bacin rana

- Sojojin Ruwan Najeriya ne suka damke su yayin da suke kokarin fara hakellar tasu

- Yanzu haka an kama jirgin da kayan da suka dauko kuma sun sun shi hannu

Rundunar sojin ruwar kasar nan ta yi nasarar cafke wani jirgin fasa kwauri makare da buhun Shinkafa har 2,860, 'yar kasar waje wadda darajar kudinta zai kai kimanin Naira Miliyan N50m tare da wasu mutane biyar da ake zargin su ne wanda suka shigo da ita.

Shugaban tawagar Rundunar sojin ruwan Julius Nwagu ya ce sun kai sumamen ne tare da hadin guiwar hukumar hana fasa-ƙauri ta garin Calabar a ranar Labara, bayan samun wasu bayanan sirri da suka yi.

Sojojin Ruwa sunyi gagarumar nasarar kama shinkafa har buhu 2,860 daga wajen ‘yan fasa kwauri
Sojojin Ruwa sunyi gagarumar nasarar kama shinkafa har buhu 2,860 daga wajen ‘yan fasa kwauri

KU KARANTA: Rikicin Duniya: Wani Malami mai wa’azi ya damfari ‘Dan Canji N12m amma ambayar da shi beli a N5m

A cikin wani jawabi da aka fitar Mr. Nwagu ya ce"Mun samu labarin zuwan jirgin hakan ta sa muka baza jami'anmu a ko ina, duhu na fara yi kawai sai muka hango wadannan mutane su biyar inda suka fito da zummar kwashe dukkan shinkafar daga cikin jirgin zuwa wasu kananan jiragen ruwa da niyyar kai su maɓoya, wato inda suke ɓoye dukkan irin wannan kayan na fasa-kauri.

"Yanzu haka mun kama su sannan mun kwashe komai haka zalika zamu cigaba da bincike". Nwagu ya bayyana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel