Dalilin da yasa na kashe budurwata – Adamu Isa

Dalilin da yasa na kashe budurwata – Adamu Isa

Kwamishanan yan sandan jihar, Abdulmaliki Sumonu, ya tabbatar da damke Muhammad Adamu, wanda ya hallaka budurwarsa, Hauwa Muhammad, yar shekara 24.

Abdulmaliki Sumonu ya bayyanawa manema labarai a Damaturu ranan talata cewa Adama da shekara 30 ya bayyanawa hukuma.

Kwamishana yace: “Ina farin cikin sanar muku cewa wadanda ya aikata kisan Hauwa Muhammad ranan 29 ga watan Mayu, ya shiga hannu.”

Shugaban yan sanda ya baiwa Adamu daman bayyanawa jama’a dalilin da yasa ya aikata wannan abun takaici.

KU KARANTA: Maza ayi hattara: Yadda wata Malama ta burma ma Maigidanta wuka daga cacar baki

Adamu yace: “ Suna na Muhammad Isa Adamu daga karamar hukumar Potiskum. Na fara soyayya na Hauwa a shekarar 2014, ta kasance mai biyayya gareni."

"Na kasance mai ta'amuni da muggan kwayoyi kusan shekaru biyar yanzu. Na yi iyakan kokarina wajen gamsar da iyayena domin su kai gaisuwa gidansu Hauwa amma suka kiya.”

Kawai kafin in farga, sai wani ya fara soyaya da ita. Farkon samun matsalanmu kenan. Tace idan iyayena ba zasu kawo gaisuwa ba, in bari wani ya shiga.”

“Wata ranan ban san me ya shiga kai na ba, sai na sha kwaya kuma na tafi kasheta da kashe kaina. Na kasheta da wuta.”

Adamu yace ya bai dade da kamala karatunsa a kwalejin ilimin fasaha na Potiskum ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng