Karanta mummunan matsalar da shan kwaya ya janyo tsakanin Saurayi da Budurwa

Karanta mummunan matsalar da shan kwaya ya janyo tsakanin Saurayi da Budurwa

Rrundunar Yansandan jihar Yobe ta sanar da cafke wani matashi mai shekar 30,Muhammad Isa Adamu da laifin kisan budurwarsa, Hauwa Muhammad ta hanyar yi mata yankan rago, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamishinan Yansandan jihar, Abdulmaliki Sunmonu ne ya bayyana haka a yayin da yake nuna ma yan jaridu wanda ake zargin, a ranar Talata, 5 ga wata Yuni, inda yace tuni mutumin ya tabbatar da aikata laifin.

KU KARANTA: Babu wanda ya isa ya tsige Buhari matukar ina raye – Inji Gudaji Kazaure

Kwamishinan yace: “Adamu yace ya gayyaci budurwar tasa ne zuwa wani waje dake bayan hukumar RUWASA, inda ya umarceta da ta rufe idanunta da nufin zai yi mata kyautar ban mamaki, kwatsam sai ya gigara mata wuka a wuya, nan take ta fadi matacciya, inda ya dauke gawar ya boye.”

Bugu da kari, kwamishina Sunmonu yace Isa da Hauwa sun shafe tsawon shekaru uku suna soyayya, amma sai ga shi abin bakin ciki ya kasheta a ranar 29 ga watan Mayu.

Shima dayake tattaunawa da manema labaru, Isa ya tabbatar da laifinsa, inda yace kishi ne ya kwashe shi ya aikata kisan budurwarsa, ya kara da cewa ya aikata hakan ne yayin dayake cikin maye. Sai dai yace yayi yayi a aura masa Hauwa, amma iyayensa suka ki.

“Daga baya sai naga wani saurayi ya fara zuwa wajenta, da na tambayeta mai yasa haka, sai tace min idan iyayena ba zasu bari na aureta ba, na kyaleta ta auri wanda yake sonta da aure, daga nan sai na rasa abindake damuna, inda na afa kwayoyin Exol, na yanke shawarar na kasheta na kashe kaina.” Inji shi

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng