Hotuna: Shugaba Buhari ya sha ruwa da manyan Malamai da sarakuna
Shugaban kasa Muhammadu Buharu ya shirya liyafar shan ruwa ga sarakunan gargajiya da manyan malamai a yau Talata, 5 ga watan Yuni 2018 a fadar shugaban kasa dake birnin tarayya Abuja.
Daga cikin wadanda suka halarta sune Ooni of Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi Ojaja II, sarkin Gwamndu, Alhaji Muhammad Bashaar; Etsu Nupe, maimartaba Alhaji Yahaya Abubakar.
Sauran sarakunan sune Ofo of Umuofor Kingdom Eze Abdulfatah Chimaeze Emetumah III, Oba of Lagos, Oba Rilwan Akiolu.
Daga cikin malaman da suka halarta sune shugaban hukumar NITDA, Dakta Isa Ibrahim Ali Fantami; Babban limamin masallacin tarayya, Farfesa Galadanci; shugaban kungiyar Izalataul Bid'a wa ikaamatus sunnah JIBWIS, Shaykh Abdullahi Lau.
Sauran sune sakataren kungiyar Jama'atu Nasril Islam, Dakta Khalid; Shaykh Yakubu Hassan Katsina Sautus Sunnah; shakyk Abubakar Gero Argungun.
KU KARANTA: Labarin yadda wasu Musulmai ke karyar azuminsu don abin Duniya
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng