Yanzu Yanzu: Daraktan Kogi ya fadi ya mutu a Ofis
Wani mataimakin darakta a ma’aikatar ilimi na jihar Kogi, Mista Haruna David, ya fadi ya mutu a Ofishinsa a ranar Talata, 5 ga watan Yuni.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta tattaro a Lokoja cewa David ya fadi da misalin karfe 3 na rana.
Anyi gaggawan kai shi babban asibitin tarayya, Lokoa, inda anan likitoci suka bayyana mutuwarsa.

Marigayin ya fito daga Ogugu, karamar hukumar Olamaboro sannan kuma ya kasance shugaban kungiyar manyan ma’aikatan Najeriya sannan kuma shine shugaban kungiyar cigaban Ogugu shiyar Lokoja.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Ana nan ana tattara sa hannu don tsige shugaba Buhari a yanzu haka – Dan majalisa
Jami’in labarai na ma’aikatar ilimi, Alhaji Seidu Adamu, ya tabbatar da lamarin amma ya kasa ci gaba da sharhi sakamakon dimuwa da ya shiga.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng