Yanzu-yanzu: Sai mun tsige Buhari face ya cika sharruda 10 – Yan majalisa bayan ganawarsu
Yan majalisan wakilai da dattawa sun lashi takobin tsige shugaba Muhamadu Buhari face ya cika wasu sharruda goma da suka kindaya masa.
Bayan ganawar da yan majalisan sukayi a yau wanda ya kwashe akalla sa’o’I 4, yan majalisan sun yanke shawaran cewa za su tsige shugaban da karfinsu idan har bai cika wadannan sharruda 10 ba.
Sharrudan sune,:
1. A baiwa hukumomin tsaro umurnin kawo karshen kashe-kashen da ke faruwa a fadin kasa.
2. Cin mutuncin yan adawan da fadar shugaban kasa keyi ya isa hakan kuma kada ya sake faruwa
3. Wajibi ne bangaren zantarwa su bi doka
4. Za’a daurawa shugaban kawa alhakin dukkan abinda wadanda ya nada suka yi
5. Gwamnatin tarayya ta nuna gaskiya wajen yaki da rashawan da takeyi
6. Wajibi ne a karewa majalisar dokoki hakkinsu kuma ayi binciken wadanda suka sace sandar majalisa
KU KARANTA: Ya kamata yan Najeriya su nemi sanin kudaden da ake kashewa Gwamnoni da shugaban kasa – Shehu Sani
7. Majalisar dokoki za ta hada kai da majalisar ECOWAS, EU,UN da yan kungiyoyin fafutuka wajen kare demokradiyyan Najeriya
8. Wajibi ne a kawo karshen rashin aikin yi a Najeriya
9. Wajibi ne a ja kunne kuma a caccaki sifeto janar na hukumar yan sanda
10. Wajibi ne a jinjinawa shugaban majalisan dattawa, Bukola Saraki da kuma kakakin wakilai, Yakubu Dogara.
Yan majalisan sunce face an cika wadannan sharruda, ba zasu dagawa bangaren shugaban kasa kafa ba.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng