Kalli yadda ake rabon abinci karkashin tsarin ciyar da yara na gwamnatin tarayya a wata makarantar firamarin Jihar Kano

Kalli yadda ake rabon abinci karkashin tsarin ciyar da yara na gwamnatin tarayya a wata makarantar firamarin Jihar Kano

A yayin da Gwamnatin Tarayyar Najeriya ke cewa, shirinta na ciyar da dalibai a wasu daga cikin makarantun firamare na kasar na kara alkaluman daliban da ke zuwa makaranta.

Masu bibiyar aiwatar da shirin na cewa, wani nau’in abincin da ake bai wa daliban hadari ne ga lafiyar su.

An gano daliban wata makarantar Firamare dake jihar Kano na cin abinci akan takardan rubutu inda hakan ya janyo sharhi a yanar gizo. Kafar yada labarai ta Voice of America (VOA), Hausa ce ta saki bidiyon a ranar Litinin 4 ga watan Yuni.

Kalli yadda ake rabon abinci karkashin tsarin ciyar da yara na gwamnatin tarayya a wata makarantar firamarin Jihar Kano
Kalli yadda ake rabon abinci karkashin tsarin ciyar da yara na gwamnatin tarayya a wata makarantar firamarin Jihar Kano

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin tawagar majalisar Dinkin Duniya (hotuna)

Da aka tambayi dalilin da ya sa ake ciyar da daliban abinci akan takarda, malaman wadanda suka nemi a boye sunayensu sun ce gwamnatin tarayya tayi alkawarin aiko da kwanuka nan ba da jimawa ba.

Ga bidiyon a kasa:

Idan dai bazaku manta ba shirin ciyar da dalibai na daga cikin alkawaran da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari tayi a lokacin yakin neman zabe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel