Asirin wani Miji da yake sadadawa dakin ‘yar aikin gidansa ya tonu
- Miji da Mata sun gurfana gaban Kotu bisa zargin juna da cin amana
- Tun da fari Matar ce ta kai shi kara domin a raba auren nasu
- Amma sai dai ashe shi ma abin na ransa don haka kawai ya ce Alkalin ya biyamata bukatarta
Wata mata mai shekaru 36 da haihuwa ta gurfanar da mijinta a gaban wata kotu dake garin Legas domin kotun ta raba aurensu bayan shafe shekaru 10 suna tare bisa dalilin halin mai gidan nata na yawan san mata.
Matar mai suna Mrs. Florence Asanyi wadda 'yar kasuwa ce ta bayyanawa kotun hakan ne a yau Laraba inda take rokon kotun da ta raba auren na su.
Ta sanar da kotu cewa mijin nata an sha kama shi da laifuka daban-daban na bin matan wasu, amma hakan bai hana shi bin dare ya shiga dakin 'yar aikin gidan su dan yin lalata da ita ba.
Matar ce "Mijina manemin mata ne domin ba sau daya ba na sha kama shi yana lalata da yar aikin gidanmu a cikin dakinta".
"Akwai wata makociyarmu ta taba zuwa ta kawo min kashedin mai gidana cewar na ja masa kunne ya daina neman 'yarta".
"Kuma na taba kama shi hannu biyu yana shan maman wata 'yar uwata, amma ban ce masa komai ba baya ga haka ga neman kawayena da yake yi".
"Da akwai lokaci da yace min idan na cika takura masa zai sa min guba a abinci domin na ci na mutu. Wata rana ya kawo min abinci bayan na gama ci sai na fara jin zafi a cikina, sai amai ya biyo baya nan take na tafi asibiti wanda ba shi da nisa da mu, kuma aka tabbatar min da cewar na ci guba ne a abincin da naci".
KU KARANTA: Shari'a sabanin hankali: An tura su gidan kaso na wata tara-tara saboda sun saci wayar wuta
Lauyan dake kare mai karar ya ce Maigidan matar ya mayar da ita tamkar jaka banda duka da zagi ba abinda yake mata, ga cin mutunci da zarafi.
Wanda ake karar mai suna Stanley, ya bayyanawa kotu cewa bai yarda da matar tasa ba saboda yana zarginta da cin amanarsa wajen kwanciya da wani namijin.
Ya ce "A watanJanairun 2017 wata rana ta shigo gida da wata mota wadda darajar kudinta ya kai Naira Miliyan daya na tambayeta a ina ta samu kudi ta saya amma tace min wai da kudinta ta saya, wanda ni kuma ban yarda ba saboda nasan kayayyakin abinci take sayarwa kuma jarinta bai kai karfin da zai iya saya mata motar ba".
Ya cigaba da cewa, "Wata rana na dawo daga aiki na tarar ta kwashe kayanta baki daya da yaranmu ta tafi da su daga bisani ta turo min da sakon kar ta kwana cewa ita yanzu ta koma gidan sabon masoyinta, kuma dama mutane da dama sun sha kawo min maganarta cewa ana ganinta a otel daban-daban da maza.
Amma ban taba yarda ba saboda bana son wani abu ya shiga tsakanina da ita, na kira wayarta lokuta da dama amma taki amsawa, sai daga bayane ta kirani take sanar dani cewa yaron mu na uku da muka haifa ba nawa bane na mutumin da suke tare ne".
Daga karshe dai wanda ake tuhumar ya cewa kotu shi baya bukatar komai face kotu ta cikawa matar tasa burinta na a raba auren nasu.
Amma alkalin kotun ya basu damar su je su sasanta kansu zuwa nan da 3 ga wata mai kamawa kafin a yake hukunci.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng