Ya kamata yan Najeriya su nemi sanin kudaden da ake kashewa Gwamnoni da shugaban kasa – Shehu Sani

Ya kamata yan Najeriya su nemi sanin kudaden da ake kashewa Gwamnoni da shugaban kasa – Shehu Sani

Shehu Sani, Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisar dokokin kaasar ya yi kira ga yan Najeriya da su nemi sanin adadin kudaden da ake kashewa gwamnoni da shugaban kasa.

Sanatan wanda yayi wannan kira yayinda yake Magana akan hanyar tafiya 2019, wani shiri da gidan talbijin din Channels ta shirya yace hujjar shin a bayyana yawan kudin sanatoci ya rufe fagen bukata da mutane ke yi na son sanin albasin yan majalissun tarayya.

Da yake dasa ayar tambaya akan kudaden ministoci, da gwamnoni, Shehu Sani yace: “Bai kamata ayi lullubi a ofishin gwamnati ba, don haka yanzu dayan Najeriya suka san albashin yan majalisar dokoki, ya kamata su san na ministocinmu; nawa ne albashin gwamnoni?

Ya kamata yan Najeriya su nemi sanin kudaden da ake kashewa Gwamnoni da shugaban kasa – Shehu Sani
Ya kamata yan Najeriya su nemi sanin kudaden da ake kashewa Gwamnoni da shugaban kasa – Shehu Sani

“Nawa ake kashewa shugabannin gwamnati? Nawa ne na hadiman shugaban kasa, hadimai da kuma mutane dake kewaye da gwamnati? Sannan kuma nawa ake kashewa shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa?"

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari, Osinbajo sun gana da shugabannin tsaro

Idan zaku tuna a watan Maris ne dai sani ya tada wata kura bayan ya bayyana yawan kudaden da sanatoci ke karba a matsayin albashi da sauran alawus dinsu wanda ya kai naira miliyan 13.5 ko wace wata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel