Manyan fashin kurkuku 10 da ya faru a Najeriya
Yayinda akayi mumunar fashin gidan yari Minna, jihar Neja a jiya, jaridar Legit.ng hausa ta kawo manyan irin wadannan fasa kurkuku da ya faru a Najeriya.
1. Kurkukun jihar Bauchi
An fasa kurkukun jihar Bauchi a watan Satumban 2010 wanda shine mafi girma a tarihi da aka sani inda fursunoni 721 suka arce daga gidan yarin.
2. Kurkukun Ogun
An fasa kurkukun jihar Bauchi a watan Junairun 2013 inda fursunoni 20 suka arce amma an damke 4 daga cikinsu.
3. Kurkukun Ondo
An fasa kurkukun jihar Ondo a watan Yunin 2013 inda fursunoni 175 suka sha amma an damko 54 daga baya.
4. Kurkukun Legas
An fasa kurkukun jihar Legas a watan Oktoban 2014 inda fursunoni 12 suka arce.
5. Kurkukun Kogi
An fasa kurkukun jihar Kogi a watan Nuwamban 2014 inda fursunoni 144 suka arce amma an damke 45.
6. Kurkukun jihar Ekiti
An fasa kurkukun jihar Ekiti a watan NUwamban 2014 inda fursunoni 341 suka arce amma an damko 67
7. Kurkukun jihar Neja
An fasa kurkukun jihar Neja a watan Disamban 2014 inda fursunoni 270 suka tsira
KU KARANTA: An kai Saraki da Mataimakinsa kara Kotu a dalilin IGP Ibrahim Idrsi
8. Kurkukun jihar Yobe
A ranan 4 ga watan Yuni 2012, yan Boko Haram sun fasa kurkukun Jimeta dake Damaturu domin tsiratar da abokansu. Yan Boko Haram 40 sun arce, an kashe 7.
9. Fashin kurkukun DSS Abuja
A watan Maris 2014, yan Boko Haram sun kai hari kurkukun hukumar DSS domin tsiratar da mambobin kungiyar. An samu nasarar kashe 21.
10. Kurkukun Minna
A jiya, an fasa kuukun Minna inda akalla fursunoni 200 sun arce. A yanzu, jami’an tsaro sun baama neman wadanda suka gudu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng