Shugaban kungiyar Izala Bala Lau ya kaddamar da muhimman ayyuka 3 kafin goman karshe na Ramadan (hotuna)

Shugaban kungiyar Izala Bala Lau ya kaddamar da muhimman ayyuka 3 kafin goman karshe na Ramadan (hotuna)

Rahotanni sun kwo cewa Shugaban kungiyar Izala na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya kai ziyara gidajen Fursunoni biyu dake jihar Adamawa.

Shugaban wanda ya fara da ziyartan gidan Fursunan Yola ta kudu yace sun fito ziyarar ne domin duba halin da masu laifi ke ciki, da kuma taimaka musu a wurin da hakan zai yuwu.

Sheikh yace: "Hakika amfanin malamai shine wa'azi da karantar da tarbiyya, wajibi ne a sami wannan a cikin gidan nan. Idan da zaka daure mutum na shekaru 100 amma baka yi mishi wa'azi ka sauya tunanin sa ba, to tamkar aikin banza ne kayi."

Da yake jawabi, shugaban gidan fursunan na Yola ta kudu Abdullahi Baya yace babu kungiya da take kokarin kula da gidajen kaso kaman kungiyar Izala. A saboda haka ya jinjina wa Sheikh Bala Lau da ziyarar ta sa. Ya kuma yi alkawarin cigaba da bada hadin kai ga malamai a gidan.

Shugaban kungiyar Izala Bala Lau ya kaddamar da muhimman ayyuka 3 kafin goman karshe na Ramadan
Shugaban kungiyar Izala Bala Lau ya kaddamar da muhimman ayyuka 3 kafin goman karshe na Ramadan

Daga nan ne tawagar Sheikh Bala Lau ta wuce masallacin Daubeli, inda shugaban ya kaddamar da mika kayan tallafi ga marayu.

Shehin malamin a jawaban kaddamarwa ya ambaci falalan da mai taimakawa maraya zai samu a wurin Allah. Saboda haka yayi kira ga al'umman musulmai a duk inda suke su taimakawa marayu.

Shugaban kungiyar Izala Bala Lau ya kaddamar da muhimman ayyuka 3 kafin goman karshe na Ramadan
Shugaban kungiyar Izala Bala Lau ya kaddamar da muhimman ayyuka 3 kafin goman karshe na Ramadan

Sheikh ya kaddamar da mika kayan tallafin ga marayu guda shida, inda ya mika musu tallafin su da hannun shi.

Daga bisani Tawagar Shugaban ta wuce babban masallacin Fada a Yola, inda Sheikh ya halarci sallan janaiza na wata baiwar Allah mahaifiyar daya daga cikin abokan sa.

KU KARANTA KUMA: APC ce za ta ci gaba da mulkin Najeriya har illa ma sha Allah - Mama Taraba

Daga nan tawagar Sheikh ta dugunzuma zuwa gidan Fursunan Yola ta Arewa, inda nan ma ya bada shawarari ga shuwagabannin gidan.

Shugaban kungiyar Izala Bala Lau ya kaddamar da muhimman ayyuka 3 kafin goman karshe na Ramadan
Shugaban kungiyar Izala Bala Lau ya kaddamar da muhimman ayyuka 3 kafin goman karshe na Ramadan

A daya bangaren kuma, Sheikh Bala Lau ya rufe tafsirin sa na Ramadaan wanda yake gabatarwa a masallacin Daubeli, Jimeta-Yola bayan shafe kwanaki 19 na Ramadan. Sheikh yace rufe tafsirin ya biyo bayan uzurin shugabancinc Al'umma. Saboda haka ne ma ya wakilta Sheikh Ali Mamman ya cigaba da gudanar da tafsirin zuwa karshen Ramadan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel