Soyayya ko son kudi: Wata sambaleliyar budurwa ta auri bature dan shekara 90
A wani yanayin shauki mai tattare da tsananin nuna kauna, wata sambaleliyar budurwa, bakar fata, 'yar asalin kasar Ghana da ke wa kanta lakani da Ashlorm TheZionist ta ruda kafafen sadarwar zamani na dan wani lokaci biyo bayan wasu hotunan ta da ta saki na auren da ta yi.
A cikin hotunan dai budurwar ta nuna kanta ne tare da wani tsohon bature mai kimanin shekaru 90 a duniya da ta ce sabon angon ta ne.
KU KARANTA: Wata 'yar Kano ta aure baturen Amurka (Hotuna)
Legit.ng ta samu cewa sai dai hakan ke da wuya sai jama'a da dama suka cigaba da turuwa suna fadar kalaman batanci gareta inda suke cewa wannan ba soyayya bace kawai son kudi ne tsabar sa.
Amma ita kuma budurwa hakan bai sa ta saduda ba inda ta mayar wa da wani raddi tana mai cewa: "Allah ne kadai zai yi mani hisabi ba wani katon banza ba don haka ban damu ba".
Haka ma budurwar tayi ta kwararawa mijin nata albarka inda ta ce tabbas tayi dace da miji na gari.
dan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng