Kaico! Yadda wani Direban bankaura yayi ajalin wata budurwa amaryar gobe
Rundunar Yansandan jihar Legas ta maka wani direban bankaura Atek Benjami mai shekaru 52 gaban kuliya manta sabo sakamakon tuhumarsa da take yi da yin sanadin mutuwar wata budurwa, Destiny Yahaya dake gab da amarcewa.
Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito Yansanda na tuhumar Direban da laifuka guda biyu da suka hada da tukin ganganci, da kuma yin sanadin mutuwar dan Adam, a gaban Kotun Majistri dake Ikeja na jihar Legas.
KU KARANTA: Wani dan majalisa ya sanya tukuicin N5,000,000 ga duk wanda ya yanko masa gashin Shehu Sani
Dansanda mai shigar da kara, Sufeta Benson Emuerhi ya bayyana ma Kotu cewa a ranar 24 ga watan Mayu da misalin kerfe 8:30 na dare ne direban ya banke Destiny a yayin tukin ganganci akan titin Kunle Akinosho dake unguwar Oshodi na jihar Legas.
“A lokacin da Benjamin yayi kokarin juya motarsa kirar motar Bus dake da lamba KTU 823 XW ta baya yayin da yake kan gudu ne ya kade Destiny mai shekaru 23, inda ta samu rauni akanta, amma daga bisani aka tabbatar da mutuwarta a Asibti.” Inji Dansanda Emuerhi.
A cewar Dansandan, laifukan sun saba ma sashi na 167 (1) da na 20 na dokokin tuki na shekara ta 2012 na jihar Legas, sai dai Direban bankaurar ya musanta tuhume tuhumen gaba daya.
Bayan sauraron dukkanin bangarorin, sai Alkalin Kotun, Sule Amzat ta bada belin Direban akan kudi naira dubu hamsin, tare da mutane guda biyu da zasu tsaya masa akan N50,000, sa’annan daya ya kasance dan uwansa ne na jinni, daga karshe ta dage karar zuwa ranar 30 ga watan Yuli.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng