‘Yan sanda sun bazama neman Fursinoni 200 da suka tsere daga gidan Yari a Minna

‘Yan sanda sun bazama neman Fursinoni 200 da suka tsere daga gidan Yari a Minna

- Bayan tserewa da Fursinoni su kayi, yanzu haka ana lalubensu kamar bataccen guga a rijiya

- Gidan Yarin dai an kai masa hari ne a jiya Lahadi, lamarin da wasu ke ganin kamar Maharan sun je kubutar da 'yan Uwansu masu laifi ne

'Yan sanda a jihar Naija sun shaida cewa a yau Litinin sun fara daukar matakan zabaro Mutane 200 da suka arce jiya daga wani gindan Yari mai matsakaicin tsaro a Minna ta jihar Naija.

Kwamishinan ‘Yan sanda na jihar Dibal Yakadi, a wata hira da manema labarai ya tabbatar da cewa Firsunoni 19 ne kacal dag cikin 219 suka kai ga kamawa kafin su tsere “Muna aiki tare da sauran hukumomin tsaro a jihar don ganin mun tabbatar da kamo wadanda suka tsere”.

‘Yan sanda sun bazama neman Mutane 200 da suka tsere daga gidan Kurkukun Minna
‘Yan sanda sun bazama neman Mutane 200 da suka tsere daga gidan Kurkukun Minna

"’Yan sanda yanzu haka sun fara binciken kwakwaf na ababen hawa da kuma baza jami’an sintiri na kafa domin kamo gudaddun ‘yan Fursinan." A cewar Yakadi.

Sannan kuma ya ce sun aike da wasu jami’ai zuwa tashohin Motoci dake jihar domin kama duk wadanda ke shirin barin garin, a don haka ne yayi kira ga jama’a da su taimaka musu da duk wasu bayanai da zasu taimaka wajen kamo duk wadanda suka tsere din.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa wasu Tsagerun Mahara ne suka kaiwa gidan Kurkukun hari a jiya Lahadi suka kashe wani Ma’aikaci guda da yake bakin aiki a lokacin da kuma wani da yazo wucewa a babur, wanda hakan ya baiwa Fursinonin damar tserewa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng