IGP Idris ya samu yardan Buhari wajen kama Saraki akan kisan Kwara

IGP Idris ya samu yardan Buhari wajen kama Saraki akan kisan Kwara

- Shugaba Buhari ya yarje ma yan sanda kama shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki

- Buhari ya jadadda cewa babu wanda ya fi karfin hukuma a kasar

- Ana zargin Saraki da hannu a kisan Kwara

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace bai da ja a ko wani shiri da hukumar yan sanda keyi na kama shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki akan lamarin kisan jihar Kwara, jaridar Premium Times ta ruwaito.

A ranar Juma’a da rana ne shugaban kasar ya karbi bakuncin sufeto janar Ibrahim Idris a fadar shugaban kasa, inda anan ne ya fada masa cewar akalla makasa 20 ke da nasaba da Saraki a jiharsa, acewar wasu majiyoyi.

Majiyoyisun bayyana cewa shugaban yan sandan ya isa fadar shugaban kasa da takardun binciken wanda ke da nasaba da Saraki. Ana iya kama babban dan majalisa a ko wacce rana bayan cewa da shugaban kasar yayi ya ba doka damar aiwatar da duk wai abun day a kamata domin gano masu laifi.

Tun da farko dai rundunar 'yan sandan ta tabbatar da cewa ta kama mutane biyar daga cikin 'yan fashin kuma sun yi ikirarin cewa Saraki da kuma Gwamnan Kwara, Abdulfatah Ahmed suka dauki nauyinsu. An yi amfani da motar Madugun 'yan fashin mai suna Ayoade Akinnibosun, mai shekaru 37, ne wanda kuma a lambar motar akwai sunan Saraki.

IGP Idris ya samu yardan Buhari wajen kama Saraki akan kisan Kwara
IGP Idris ya samu yardan Buhari wajen kama Saraki akan kisan Kwara

Daga cikin jami'an gwamnatin jihar Kwara da ake tuhuma da hannu a fashin bankin akwai Shugaban ma'aikatan Fadar gwamnatin jihar Kwara, Yusuf Abdulwahab.

KU KARANTA KUMA: Duk miji da matan da basu san namban sirri na katin ATM din junansu ba toh ba ma’aurata bane – Mataimakin kwamishinan yan sanda

Tuni dai humumar 'yan sanda ta tura sakon gayyata ga Saraki dominn yin bayani game da zargin da ake yi masa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku neme mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng