Cigaba da tsare Zakzaky da Gwamnatin Buhari ke yi rashin adalci ne - Buba Galadima
Tsohon babban na hannun damar shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari kuma fitaccen dan adawa Injiniya Buba Galadima ya bayyana cigaba da tsare jagoran 'yan shi'a a Najeriya Ibrahim Zakzaky da gwamnatin tarayya ke ci gaba dayi a matsayin rashin adalci tsagwaron sa.
Injiniya Buba Galadima ya bayyana hakan ne a yayin da ake fira da shi a gidan talabijin mai zaman kan sa na AIT a wani shiri da ake cewa "Focus Nigeria: Matters Arising" lokacin da aka tambaye shi ra'ayin sa game da cigaba da tsare shi.
KU KARANTA: Gaskiyar magana shekaru 4 sun yi mana kadan - Osinbajo
Legit.ng ta samu cewa shi dai Buba Galadima ya bayyana cewa shi a ganin sa ana cigaba da tsare Zakzaky din ne saboda kawai irin akidar sa ta sha banbab da wadda mafiyawa daga jami'an gwamnatin ke yi.
A wani labarin kuma, Mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa a hakikanin gaskiya, shekaru hudu kacal sun yi kadan ga dukkan wani shugaba a Najeriya indai ana so ya kawo sahihin canji mai ma'ana a kasar.
Farfesa Osinbajo ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabin sa na a wajen taron karawa juna sani da gidan jaridar nan na Financial Times ya shirya a garin Legas.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng