Sojojin Najeriya sun fara sharar Daji don gamawa da masu aikata laifi
- A yunkurin Sojoji na tabbatar da wanzuwar tsaro sun bullo da wani sabon salo na yaki da masu laifi
- Rundunar Sojoji ce ta bayyana haka domin magance yawaitar satar Mutane da kuma fashi da Makami
- Daga fara aikin nasu har sun samu nasarar samun wata gawa
Rundunar Sojojin Najeriya ta Bataliya 32 ta bayyana fara sharer Daji a karamar hukumar Efon Alaaye dake jihar Ekiti.
Fara wannan sharar dai ya biyo bayan yunkurin rundunar na magance yawaitar aikata manyan laifuka irinsu fashi da makami da kuma garkuwa da Mutane a yankin. Babban hafsan Soja Birgediya Janar James Ataguba ya bayyana fara sumamen da safiyar ranar Juma’a.
Yanzu haka dai Sojojin sun yiwa wani Dajin mai yawan duhuwa kawanya a yankin Arifa dake kan Titin Iwaraja domin yi wa masu laifin kamun kazar kuku.
KU KARANTA: 'Yan sanda sun tabbatar da wani sabon Hari kan Al'ummar Jihar Filato
A wani jawabi nasa Mataimakin Daraktan yada labarai na rundunar Manjo Ojo Adenegan ya bayyana cewa, “Yayin da muka yiwa Dajin kawanya muka kuma kutsa kai ciki, mun samu gawar wani Mutum har ta fara rubewa da muke zargin irin wadanda ake yin garkuwa da su ne, wayarsa tana ta bugawa ana kiransa. “Mun dai sanar da Rundunar ‘Yan sanda da kuma Gwamnatin jihar samun gawar.”
Daga nan ne ya kuma shaidawa mazauna yankin da kada gabansu ya fadi sakamakon ganin Sojoji da zasu keyi a yankin, suna son su magance tsagerun da suka addabin yankin. A saboda haka kow aya cigaba da aiwatar da aikinsa yadda ya saba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng