Dan Allah ka sakarwa Buhari mara yayi fitsari – Hadimar Buhari ga Dino

Dan Allah ka sakarwa Buhari mara yayi fitsari – Hadimar Buhari ga Dino

Bayan nacewa da Dino Melaye yayi kan cewa lallai sai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba majalisar dokoki hakuri akan wani furuci da aka ce shi yayi akan su, hadimar Buhari, don haka a ranar Juma’a Lauretta Onochie ta bukaci Dino da ya kyale shugaban kasa da gwamnatinsa cikin aminci.

Idan zaku tuna Dino ya bayyana cewa Buhari yace wasu yan majalisa sun shafe tsawon shekaru goma a majalisar dokokin kasar ba tare da sun yi komai ba.

Dino ya bayyana wannan furuci a matsayin cin mutunci sannan kuma ya bukaci Buhari ya ba su hakuri.

Dan Allah ka sakarwa Buhari mara yayi fitsari – Hadimar Buhari ga Dino
Dan Allah ka sakarwa Buhari mara yayi fitsari – Hadimar Buhari ga Dino

Bayan tirgjwa da Dino ya nuna kan jawabin Buhari, Onochie tace “Wata rana Dino Melaye zai gane cewa majalisar dokoki ba mallakinsa bane."

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An harbi tsohon dan majalisa, Opeyemi Bamidele a Ekiti

Sannan kuma Onochie ta bayyana a shafinta na twitter cewa Dino na bukatar gwajin kwakwalwa kafin a bashi dama a majalisar dokoki a lokacin zamansu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku bi shafukanmu domin samun labarai https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga hanyar mallakar sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel