"Yadda wata budurwar da na hadu da ita a Fesbuk da goga mun kanjamau"

"Yadda wata budurwar da na hadu da ita a Fesbuk da goga mun kanjamau"

Wani ma'abocin anfani da kafar sadarwar zamani ta Fezbuk mai suna Ola O'Neil da ke da adreshin (@_gal2) a dandalin Tuwita ya fito fili ya fadawa duniya yadda wata budurwar da yayi a kafar sadarwar zamani ta Fezbuk ta goga masa cutar kanjamau.

Mutumin dai wanda ya zayyana cewa haduwar sa da budurwar ke da wuya a kafar sadarwar zamanin cikin kasa da sati daya har sun shirya haduwa a otel inda kuma suka kwanta da juna.

"Yadda wata budurwar da na hadu da ita a Fesbuk da goga mun kanjamau"
"Yadda wata budurwar da na hadu da ita a Fesbuk da goga mun kanjamau"

KU KARANTA: EFCC ta kama wani fasto dan damfara

Legit.ng ta samu cewa daga nan ne kuma sai ya shawarci dukkan samari da 'yan mata da su yi taka tsan-tsan game da rayuwa kuma su bi a hankali kar su jefa kansu cikin nadama da na sani irin wadda ya shiga.

A wani labarin kuma, Kimanin kasa da wata daya bayan da wata daliba ta fallasa wani malamin ta a jami'ar Obafemi Awolowo University, dake jihar Osun da ya nemi ya kwanta da ita, wata budurwar ma daga jami'ar garin Legas ita ma ta kara fallasa wani malamin.

Ita dai wannan budurwar daga jami'ar Legas din wadda aka boye sunan ta saboda dalilai na tsaro ta ce sunan Farfesan da ya ci zarafin nata shine Olusegun Awonusi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel