An kamo Zakuna biyu da damusa uku sun tsere daga Gidan Zoo a kasar Jamus
Hukumomi a Jamus sun bayar da sanarwar cewa an samu nasarar kamo zakuna biyu da damusa ukun da suka gudu daga gidan ajiye namun daji wato zoo a wani yanki da ke yammacin kasar.
An gano dabbobin ne a harabar Gidan Zoo dake Lünebach bayan da aka yi amfani da jirgi maras matuki wajen bidar su.
A ranar Juma'a da safe ne 'yan sandan kasar suka bayar da sanarwar tsarewar dabbobin tare da mutane shawarar kasancewa a gidajensu, sannan kuma su kira 'yan sanda idan har suka ga wani abu.
Wani jami'i da ke yankin ya kuma shaida wa kamfganin dillancin labarai na AFP cewa wata muguwar dabba da ake kira bear ma ta tsere daga gidan namun daji na Eifel, amma an harbe ta.
KU KARANTA KUMA: "Yadda wata budurwar da na hadu da ita a Fesbuk da goga mun kanjamau"
Kafofin yada labaran Jamus sun ce dabbobin sun balle ne bayan da aka sheka ruwa kamar da bakin kwarya cikin dare, wanda ya jawo ambaliyar da ta lalata kejin da aka kange su.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku bi shafukanmu domin samun labarai https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga hanyar mallakar sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng