Kuma! An yi garkuwa da mutane 25 a hanyar Birnin-gwari, Kaduna

Kuma! An yi garkuwa da mutane 25 a hanyar Birnin-gwari, Kaduna

Bayan babban hafsan sojin Najeriya ya kafa barikin soji a hanyar Birnin-gwari a jihar Kaduna, an kuma yin garkuwa da akalla mutane 25 a hanyar.

Majiya ya bayyanawa jaridar Cable ranan Alhamis cewa masu garkuwa da mutanen sun tare hanyar kauyen Kiryoyi da Maganda a karamar hukumar birnin gwari.

Sun tare motoci sannan suka kore fasinjoji cikin daji.

Kuma! An yi garkuwa da mutane 25 a hanyar Birnin-gwari, Kaduna
Kuma! An yi garkuwa da mutane 25 a hanyar Birnin-gwari, Kaduna

Shugaban kungiyar direbobin shiyar Birnin Gwamri, Danladi Duniya, ya tabbatar da hakan a wani hirar wayan tarho. Yace: “Ba zan iya fadin hakikanin adadin mutanen da akayi garkuwa da sub a amma suna da yawa.”

Kimanin 25 ko sama da haka. Ba ni da tabbaci, amma anyi garkuwa da dukkan wadanda ke cikin motan”

“Sun tsayar da motoci 5, direba daya mai tukin motar Gulf ya tsira da kyar. Abinda muke fuskanta kenan a hanyan nan. Muna kira ga jami’an tsaro su kawo karshen wannan matsala. Mutane sun gaza zuwa gona.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng