Da dumi- dumi: An zabo sabon Mataimakin Gwamnan jihar Bauchi

Da dumi- dumi: An zabo sabon Mataimakin Gwamnan jihar Bauchi

- Sai wani ya rasa wani kan samu, sauran kiris jihar Bauchi tayi Angon Mataimakin Gwamna

- A satin da ya gabata ne tsohon Mataimakin Gwamnan jihar ya sauka daga kujerarsa

- Bisa wasu dalilai na kashin kansa da ya bayyana

Biyo bayan ritayar tsohon Mataimakin Gwamnan jihar Bachi Nuhu Gidado yanzu haka wata majiya mai karfi daga fadar Gwamnatin ta bayyana cewa tuni Gwamnan jihar Mohammed Abdullahi Abubakar ya mika sunan shugaban Ma’aikata na jihar Audu Sule Katagum ga Majalisar Dokokin jihar domin tabbatar da shi.

Da dumi- dumi: An zabo sabon Mataimakin Gwamnan jihar Bauchi
Gwamnan jihar Mohammed Abdullahi Abubakar
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Mataimakin gwamnan jihar Bauchi ya yi murabus daga kujeransa

Sai kuma Majalisar Dokokin jihar ta tafi hutu, amma bisa bayanan da majiyarmu ta samu ya nuna cewa ‘yan Majalisar zasu katse hutun nasu gami da dawowa bakin aiki na wani dan taki domin su fara zama a yau Juma’a don duba wasikar da Gwamnan jihar ya tura musu dake kunshe da wanda yake son maye gurbin tsohon Mataimakin nasa da shi.Kamar yadda Jaridar Tribune ta rawaito

Tsohon Mataimakin Gwamnan Nuhu Gidado ya dai sauka ne a Larabar makon da ya gabata bisa radin kansa.

Da dumi- dumi: An zabo sabon Mataimakin Gwamnan jihar Bauchi
Da dumi- dumi: An zabo sabon Mataimakin Gwamnan jihar Bauchi

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng