Kochin Real Madrid Zinedine Zidane ya ajiye aikinsa

Kochin Real Madrid Zinedine Zidane ya ajiye aikinsa

- Real tayi mummunan rashi na mai horas da ita a yau Alhamis

- Mai horas da kungiyar Zidane dai ya kafa tahirin da aka dade ba'a taba irinsa ba a kungiyar da ma tarihin kwallon kafa baki daya

Mamaki ya mamaye Duniyar ƙwallon ƙafa a yau Alhamis tun bayan da Mai horas da ƙungiyar ƙwalon ƙafa ta Real Madrid Zinedine Zidane ya sanar da hukuncinsa na barin ƙungiyar.

Kochin Real Madrid Zinedine Zidane ya ajiye aikinsa
Kochin Real Madrid Zinedine Zidane ya ajiye aikinsa

Zinedine Zidane dai ya bayyana wannan hukuncin ne yayin wani taron manema labarai, sai dai har yanzu babu wani taka maiman dalilin da yasa ya ajiye aikin. Sai kawai ya ce ƴan wasan suna da bukatar sabuwar muryar mai horaswa.

Sai dai "Ya bayyana cewa samun nasarar lashe gasar LaLiga ta kakar wasannin shekarar da ta gabata shi ne babban abinda da yake tutiya da shi."

KU KARANTA: Hattara mata: Daga haduwa a Facebook wata budurwa ta rasa budurcinta a hannun wani Kato

"Bayan shekaru uku abu ne mai matuƙar wahala cigaba da horaswa, duk kuwa da cewa na lashe gasar zakarun Nahiyar Turai har sau uku." Zidane ya bayyana.

Amma ya shaida cewa shi kansa ya san abu ne mai wahala kuma da yawa ba zasu ji dadin hakan ba, tun da rabuwa ba Mutuwa ce ba.

Zai kasance a koda yaushe kusa da kungiyar don alakar zumunci, kasancewar soyayyar dake tsakaninsa da kungiyar da kuma ƴan wasanta tare da magoya bayanta.

aLatsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng