Hattara mata: Daga haduwa a Facebook wata budurwa ta rasa budurcinta a hannun wani Kato

Hattara mata: Daga haduwa a Facebook wata budurwa ta rasa budurcinta a hannun wani Kato

Mutane da dama sun sha kokawa kan rashin alfanun shafukan kafafen sadarwar zamani kamar su Facebook, Twitter, 2go, Instagram da dai sauransu, musamman a wannan zamani da tarbiya ya tabarbare.

Kamfanin dillancin labaru ta ruwaito a yanzu haka ana can ana sha kwaramniya a tsakanin wani Mutumi mai suna Ebuka Eze da iyayen wata karamara yarinya mai shekaru 16 sakamakon zarginsa da yi mata fyade, jim kadan da haduwarsu a shafin Facebook.

KU KARANTA: Akan me Hamid Ali zai dinga yi maka yakin neman zabe? – Dino Melaye ga Buhari

Dansanda mai shigar da kara, Inspekta Christopher John ya bayyana ma wata Kotun Majistri dake Ikeja na jihar Legas cewa Ebuka ya aikata laifin ne a ranar 19 ga watan Mayu a dakinsa dake gida mai lamba 25, titin Ayodele, unguwar Oshodi na jihar Legas.

“Abokinta ne a Facebook, kuma ya gayyace ta gidansa ne, inda ta amsa gayyatarsa, amma daga isanta dakinsa, sai ya tura ta kan gadonsa, inda ya rufe mata baki da pulo, ya yi mata fyade.

“Saa’nnan yayi amfani da zanin gadon ya share jinin da ya zuba a al’auranta, amma a lokacin da ta dawo gida ne sai iyayenta suka ga jinni a jikinta, a nan ne ta fayyace musu duk abinda ya faru.” Inji John.

Dansandan ya kara shaida ma Kotu cewar laifin da ake tuhumar Ebuka ya saba ma sashi na 260 na dokokin hukunta manyan laifuka na jihar Legas na shekarar 2015, don haka ya roki Kotu ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai kamar yadda doka ta tanadar.

Sai dai Alkalin Kotun, mai sharia P.E Nwaka ya bada umarnin daure Ebuka a gidan kurkukun Kirikiri, sa’annan ya aika da karar zuwa ga babban jami’in shigar da kara na jihar Legas, don samun shawara, sai ya dage sauraron karar zuwa ranar 28 ga watan Yuni.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel