Tsofaffin Gwamnoni 12 da EFCC da sanya a gaba kuma har ta ga bayan wasu

Tsofaffin Gwamnoni 12 da EFCC da sanya a gaba kuma har ta ga bayan wasu

- Za'a iya cewa kwalliya ta fara biyan kudin sabulu a yakin da Gwamnanti ke yi da yaki da cin hanci da rashawa

- Domin kuwa ya zuwa yanzu wasu daga cikin manyan Mutane dake rike da mukamai suna fuskatar hukunci

- Cikinsu har da tsoffin Gwamnoni da Sanatoci da kuma 'yan Majalisa

A yau Legit.ng ta kawo muku rahotan jadawalin sunayen manyan Mutanen da EFCC ta nunawa ba sani ba sabo da laifukan da suka aikata tare kuma da wadanda yanzu haka suke fuskantar tuhuma domin girbar abinda suka shuka.

1- Bala Ngilari

A ranar 6 ga watan Maris na shekarar 2017 ne wata babbar Kotu ta yankewa tsohon Gwamnan jihar Bala Ngilari hukuncin shekaru biyar a gidan yari bayan da ta kama shi da laifin amubazzaranci da dukiyar al'umma a wata shari'a da aka shafe sama da watanni bakwai ana yi.

Tsofaffin Gwamnoni 11 da EFCC da sanya a gaba kuma har ta ga bayan wasu
Tsofaffin Gwamnoni 11 da EFCC da sanya a gaba kuma har ta ga bayan wasu

Mai shari'a Nathan Musa ya dai samu tsohon Gwamnan da laifin bayar da kwangiloli ba bisa ka'ida ba wadanda suka hada da na siyan Motoci 25 ga kwamishinoninsa da kudinsu ya kai har Naira Miliyan N167m.

Tun farko da an zarge shi ne da aikata laifuka har guda 17, amma sai dai Kotun daukaka kara dake zamanta a Yola tayi wancakali da wancan hukuncin da a wata shari'a da mai shari'a Olayomi Falashade a ranar 10 ga watan Yuli bisa rashin gamsassun hujjojin da zasu gamsar da kotun kan zargin da ake yi masa.

2 - James Ibori

Tsofaffin Gwamnoni 11 da EFCC da sanya a gaba kuma har ta ga bayan wasu
Tsofaffin Gwamnoni 11 da EFCC da sanya a gaba kuma har ta ga bayan wasu

Tsohon Gwamnan jihar Delta shima wata Kotu a kasar Ingila ta yanke masa hukuncin shekaru 13 a gidan yari a shekarar 2012 sakamakon kama shi da laifin cin hanci da rashawa. Daga cikin Dukiyar da aka kwace daga gare shi sun hada da; gidajensa da akaiwa kimar £2.2m da wani gidan a garin Dorset da ya kai £311,000 da wani na £3.2m a kasar Africa ta Kudu.

Wasu karin kayayyakin da aka kwace hun hada da Manyan Motoci na alfarma da suka kai £600,000 da £120,000 da €407,000

Amma duk da irin wannan laifuka da aka kama shi da su da kuma tarin Dukiyar da aka kwace daga wurinsa, wata babbar Kotu a jihar ta Delta ta wanke shi bisa duk zargin da ake masa guda 170 a wata shari'a da mai shari'a Marcel Awokulehinya gabatar ranar 17 ga watan Disambar 2009.

3 - Lucky Igbinedion

Tsofaffin Gwamnoni 11 da EFCC da sanya a gaba kuma har ta ga bayan wasu
Tsofaffin Gwamnoni 11 da EFCC da sanya a gaba kuma har ta ga bayan wasu

A shekara ta 2008 tsohon Gwamnan jihar Edo Lucky Igbinedion an zarge shi da laifin wakaci-waka- tashi da dukiyar al'ummar jihar a lokacin da ya rike mukamin Gwamnan jihar na tsawon shekaru takwas.

To amma sai dai a wani yanayi mai mutukar daure kai da ya faru na sasantawa da yayi da tsohuwar shugabar hukumar EFCC Farida Waziri, tsohon Gwamnan an yanke masa watanni shida kacal a gidan yari ko kuma ya biya tarar N3.5 million a wata shari'a da aka gudanar a babbar Kotun jihar Enugu, sannan kuma aka Kotun ta umarce shi da ya dawo da Miliyan N500m da kuma wasu gidaje uku da ya siya d kudaden da ya sata da dukiyar jama'a

4 - Diepreye Alamieyeseigha

Tsofaffin Gwamnoni 11 da EFCC da sanya a gaba kuma har ta ga bayan wasu
Tsofaffin Gwamnoni 11 da EFCC da sanya a gaba kuma har ta ga bayan wasu

A ranar 26 ga watan Yuli na shekarar 2007, tsohon Gwamnan jihar Bayelsa Marigayi Diepreye Alamieyeseigha ya amsa aikata laifuka shida da ake tuhumarsa da su na cin hanci da rashawa, kuma hr aka yanke masa hukuncin shafe shakaru biyu a kurkuku bisa kowanne laifi guda, shekaru 12 kenan, amma sai dai shekarun za'a fara lissafi ne tun daga lokacin da aka fara tsare shi kimanin shekaru biyu baya.

Daga karshe a ranar 12 ga watan Maris 2013 tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan yayi masa afuwa.

5 -Orji Uzor Kalu

Tsofaffin Gwamnoni 11 da EFCC da sanya a gaba kuma har ta ga bayan wasu
Tsofaffin Gwamnoni 11 da EFCC da sanya a gaba kuma har ta ga bayan wasu

Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon Gwamnan jihar Abia Orji Uzor Kalu da kamfanin Udeh Udeogu and Slok Nigeria Limited gaban babbar babbar Kotun jihar Legas bisa zarginsu da laifuka har 34 da suka shafi wadaka da Dukiyar al'ummar jihar da suka kai Naira biliyan N3.2b.

Amma sai dai sun duk sunki amincewa da aikata laifukan baki daya.

Sai dai kuma wasu rahotannin a kwanan baya sun nuna cewa Gwamnati ta janye wadancan tuhama da ake yi masa.

KU KARANTA: Sufeton 'Yan sanda ya bayyana dalilin rashin amsa gayyatar Majalisar Dattawa

6 - Rashidi Ladoja

Tsofaffin Gwamnoni 11 da EFCC da sanya a gaba kuma har ta ga bayan wasu
Tsofaffin Gwamnoni 11 da EFCC da sanya a gaba kuma har ta ga bayan wasu

EFCC ta gurfanar da tsohon Gwamnan jihar Oyo Rashidi Ladoja gaban wata babbar Kotun jihar Legas bisa zargin halasta kudin haram da suka kai Naira biliyan N4.7b yayin da yake a matsayin Gwamnan jihar na shekaru takwas.

7 - Murtala Nyako

Tsofaffin Gwamnoni 11 da EFCC da sanya a gaba kuma har ta ga bayan wasu
Tsofaffin Gwamnoni 11 da EFCC da sanya a gaba kuma har ta ga bayan wasu

Tsohon Gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako da Dansa Sanata Abdul-Aziz Nyako tare da karin wasu Mutane Aliyu and Zulkifikk Abba suna fuskantar shari'a a babbar Kotun dake zamanta a Abuja karkashin jagorancin mai shari'a Okon Abang bisa zarginsu da laifuka 37 da suka hada da; hada baki wajen yaudara da hadin baki, satar kudaden al'umma da kuma saba dokokin aiki, tare da sama da fadi da kimanin Naira biliyan N29b.

8 - Sule Lamido

Tsofaffin Gwamnoni 11 da EFCC da sanya a gaba kuma har ta ga bayan wasu
Tsofaffin Gwamnoni 11 da EFCC da sanya a gaba kuma har ta ga bayan wasu

Tsohon Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido EFCC na zarginsa ne tare da 'ya'yansa biyu Aminu da Mustapha da kuma karin wasu Mutane biyu bisa laifuka 27.

Ana kuma zargin shi da bayar da wasu makudan kwangiloli ba tare da bin ka'ida ba.

9 - Joshua Dariye

Tsofaffin Gwamnoni 11 da EFCC da sanya a gaba kuma har ta ga bayan wasu
Tsofaffin Gwamnoni 11 da EFCC da sanya a gaba kuma har ta ga bayan wasu

EFCC ta gurfanar da tsohon Gwamnan ne gaban wata babbar Kotun dake zamanta a jihar Plateau bisa zarginsa da lai sama da fadi da N1.162b

Laifukan da EFCC take zarginsa da shi suka 21 duk wadanda suke da nasaba da halasta kudin Haram, ciki har da kudaden gyaran harkokin ruwa da suka kai N1.162b.

Kotu dai ta daga sauraran wannan shari'a zuwa 12 ga watan Yuli mai kamawa.

10- Gabriel Suswam

Tsofaffin Gwamnoni 11 da EFCC da sanya a gaba kuma har ta ga bayan wasu
Tsofaffin Gwamnoni 11 da EFCC da sanya a gaba kuma har ta ga bayan wasu

Shi ma tsohon Gwamnan Benue Gabriel Suswam tare da kwamishinan kudi na jihar Mr. Omodachi Okolobia a lokacin yana Gwamna, na fuskantar tuhuma a wata babbar Kotun Abuja.

ana dai zarginsu ne da laifuka sama da fadi na wasu makudan kudade da suka kai N3,111,008,018.51 mallakar jihar ta Benue.

10- Ahmadu Fintiri

Tsofaffin Gwamnoni 11 da EFCC da sanya a gaba kuma har ta ga bayan wasu
Tsofaffin Gwamnoni 11 da EFCC da sanya a gaba kuma har ta ga bayan wasu

Tsohon Mukaddashin Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri shi ma yana fuskantar tuhuma a gaban Kotun mai shari'a A. R. Mohammed na babbar Kotun babban birnin tarayya Abuja dake Maitama.

Ana dai zargin tsohon kakakin Majalisar jihar ta Adamawa ne da laifuka har guda biyar wadanda suka hada da; sama da fadi da Dukiyar Gwamnati. Kuma an gurfanar da shi ne tare da wani kamfanin gine-gine mai suna Mayim Construction and Properties Limited ranar 20 ga watan Yuni na 2016 ne gaban bisa zarginsu da rufda ciki kan kudin da ya kai N2.9b da kuma biyan wasu makudai don siyan gida mai lamba Plot 7, Layin Gana dake Maitama a Abuja.

11 - Ibrahim Shehu Shema

Tsofaffin Gwamnoni 11 da EFCC da sanya a gaba kuma har ta ga bayan wasu
Tsofaffin Gwamnoni 11 da EFCC da sanya a gaba kuma har ta ga bayan wasu

Tsohon Gwamnan jihar Katsina Ibrahim Shehu Shema, yana cigaba da fuskantar tuhuma tare da wasu Ma'aikata uku, Hamisu Makana da Lawal Rufai da kuma Lawal Dankaba bisa zargin wawure zunzurutun kudaden da suka kai Naira biliyan N11b.

A wata kara da EFCC ta shigar da su bisa thumar laifuka 24, yanzu haka dai Kotun da ke sauraron shari'ar ta dage zamanta zuwa ranar 12 ga watan Yuli.

12 - Ibrahim Shekarau

Tsofaffin Gwamnoni 12 da EFCC da sanya a gaba kuma har ta ga bayan wasu
Tsofaffin Gwamnoni 12 da EFCC da sanya a gaba kuma har ta ga bayan wasu
Asali: Twitter

EFCC ta gurfanar da tsohon Gwamnan Kano Malam Shekarau da tsohon ministan harkokin waje, Aminu Wali da kuma tsohon kwamishinan Ayyuka na Kano Mansur Ahmed.

Ana tuhumar su ne da laifuka shida da suka shafi halasta kudin haram da hada kuma hada baki, tuhumar da dukkansu suka musanta.

Mai shari'a Zainab Abubakar Bagi ta babbar kotu da ke unguwar Gyadi-gyadi a birnin Kano ta bayar da belinsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel