Yanzu Yanzu: An kashe mutane 8 a sabon harin Kaduna

Yanzu Yanzu: An kashe mutane 8 a sabon harin Kaduna

Akalla mutane takwas ne suka mutu yayinda wasu da dama suka jikkata a wani hari da barayin shanu suka kai kauyen Kurege dake karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna.

Kurege wani kauye ne dake iyaka da karamar hukumar Birnin gwari anda shima ake yawan kai masu hare-hare akai-akai.

Rundunar yan sandan jihar sun tabbatar da lamarin sannan sun kara da cewa suna kokari kamo maharan.

An rahoto cewa yan bindigan sun zo ne da yawa inda suka mamaye kauyen da misalin karfe 2:00 na ranar Talata.

Yanzu Yanzu: An kashe mutane 8 a sabon harin Kaduna
Yanzu Yanzu: An kashe mutane 8 a sabon harin Kaduna

Mazauna yankin sun kara da cewa yan bindigan sunyi yunkurin sace shanayen wasu makiyaya a garin. Sannan kuma lokacin da mutane suka yi kokarin hana su sai yan bindigan suka fara harbin mutanen wanda yayi sanadiyan mutuwan mutane takwas tare da jikkata wasu da dama.

KU KARANTA KUMA: Babu batun Karin albashi a watan Satumba – Gwamnatin tarayya

Daya daga cikin shugabannin yan bangan garin na daga cikin mutanen da yan bindigan suka kashe.

Sun kuma sace shanaye a harin day a dauki tsawon sa’o’i biyu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng