Yanzu-yanzu: Ministan ma'adinai ya yi murabus daga kujeranshi

Yanzu-yanzu: Ministan ma'adinai ya yi murabus daga kujeranshi

Ministan ma'adinai, Dakta Kayode Fayemi, ya yi murabus daga kujeransa domin mayar da hankali kan kada mataimakin gwamnan jihar Ekiti, Olusola Eleka, a zaben jihar Ekiti da za'a gudanar ranan 14 ga Yuli mai zuwa.

Fayemi ya mika wasikar murabus dinsa ga shugaba Muhammadu Buhari ne makonni uku da suka gabata amma a yau, 30 ga watan Mayu ne zata fara aiki.

Ministan zai yi takara kujeran gwamnan jihar ne karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) bayan ya lashe zaben fidda gwanin jam'iyyar da aka gudanar ranan 12 ga watan Mayu.

Yanzu-yanzu: Ministan ma'adinai ya yi murabus daga kujeranshi
Yanzu-yanzu: Ministan ma'adinai ya yi murabus daga kujeranshi

Ya lashe zaben da kuri'u 941 inda sauran masu takaran guda 31 suka fadi, wadanda suka dan tabuka wani abu sune, Segun Oni (Kuri'u 481 ), Kayode Ojo (Kuri'u 281), Olufemi Richard Bamisile (Kuri'u 179), Oluyede Oluwole (Kuri'u 121), da Aluko Daniel Olugbenga (Kuri'u 86).

Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya lashi takobin cewa Fayemi ya sha kasa a zaben 14 ga watan Yuli.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel