Rashin Imani: Wasu ‘yan Bindiga sun kashe Mata da Miji sun bar Jaririnsu a raye

Rashin Imani: Wasu ‘yan Bindiga sun kashe Mata da Miji sun bar Jaririnsu a raye

- Jimami da tararrabi ya samu Mutanen jihar Taraba bayan da aka kai wa wasu Ma'aurata sumame

- Harin da ya kasance mai mutukar ban tausayi, sakamakon sandiyyar mayar da wani karamin yaro Maraya

Al’ummar Wukari na jihar Taraba sun wayi gari a jiya Talata cikin jimami da alhinin wani ta’annati da wasu ‘yan Bindiga suka aikata na kashe Miji da Mata a cikin gidansu tare da barin Jaririnsu a raye shi kadai

Rahotanni dai sun bayyana cewa lamarin ya afku ne da misalin karfe 12.45am na dare, awanni kadan bayan da Maharan Makiyaya suka kai garin jalingo yayin da wasu laman Coci ke addu’a wanda yayi sanadiyyar raunata wani guda daga cikin Malaman.

Rashin Imani: Wasu ‘yan Bindiga sun kashe Mata da Miji sun bar Jaririnsu a raye
Rashin Imani: Wasu ‘yan Bindiga sun kashe Mata da Miji sun bar Jaririnsu a raye

Da yake tabbatar da faruwar harin a manema labarai shugaban karamar hukumar ta Wukari yayin zantawa da shi ta wayar tarho Hon. Daniel Adi, ya shaida cewa da misalin 12:45am suka kai harin gidan Mata da Mijin.

A cewar shugaban yankin “Ba mu san musabbin kai harin ba amma dai bayan kashe Mutanen biyu basu dauki ko da tsinke a gidan ba. Har yanzu muna cigaba da nazarin lamarin, ba mu san ko ‘yan fashi da Makami ba ne ko turo su akai ko kuma ‘yan ta’adda ne. Amma bincike zai tabbatar da komai.”

KU KARANTA: Dakarun sunyi wa wasu barayin danyen mai laga-laga bayan musayar wuta mai zafi

Wani mazaunin garin na Wukari Mr. Angyu Sabo, ya ce kisan ya faru ne a gidan Mamatan dake da tazara kadan da gidan Kurkukun Wukari dake kan Titin Wukari zuwa Ibi. Sannan ya kara da cewa irin wannan mummunan aiki abin Allah wadai ne wanda ya jefa duk fadin garin cikin rudani da dar-dar.

A don haka ne yayi kira ga jami’an tsaro da su zage damtse wajen kawo karshen irin wannan ta’addanci.

Bayan tuntubar kakakin rundunar ‘Yan sandan jihar Taraba ASP David Misal ya ce tabbas suna da labarin faruwar lamarin har ma sun fara gudanar da bincike domin ganu wadanda suka aikata wannan mummunan aiki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel