Yaki da ta’addanci: Wani dan kungiyar ta’addanci ya kashe Yansanda guda 2
Wani dan bindiga ya hallaka mutane uku a birinin Liege na kasar Belgium a ranar Talata 29 ga watan Mayu, a wani hari irin wanda yan ta’adda suka saba kaiwa wurare daban daban, kamar yadda gidna talabijin na Channels ta ruwaito.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito dan bindigar, wanda a ranar Litinin aka sako shi daga gidan Yari, ya kai harin ne da misalin karfe 9:30 na safe, a gab da wata makarantar sakandari dake cikin birnin Liege,kimanin kilomita 90 zuwa babban birnin kasar Belgium,Brussels.
KU KARANTA: Miyagun mutane sun afka makarantar Mata, sun yi ma 15 fyade sun jikkata da dama
Haka zalika bayan ya hallaka Yansandan, sai dan bindigar ya afka makarantar sakandarin Lycee Waha, inda ya yi garkuwa da wasu dalibai da malaman makarantar.
Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa wasu kwararrun Sojoji sun samu nasarar hallaka dan ta’addan a wata musayar wuta da suka kwashe tsawon lokaci suna fafatawa, wannan hari ya biyo wayan wani harin kunar bakin wake da kungiyar ta’addanci ta ISIS ta kai a shekarar 2016.
Shi ma shugaban kasar Belgium, Charles Michel ya bayyana bakin cikinsa da lamarin, inda ya taya iyalan wadanda suka rasa rayukansu jaje, da alhini.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng