'Yan kungiyar Asiri sun sheke Mutane 3 a jihar Rivers

'Yan kungiyar Asiri sun sheke Mutane 3 a jihar Rivers

- Matsalar tsaro dai har yanzu ana jika, jihar River itama ta ga ta kanta

A kalla Mutane 3 ne suka rasa rayukansu bayan da wasu ‘yan Bindiga da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar Asiri ne suka kai hari garin Ibaa dake karamar hukumar Emohua ta jihar Rivers

‘Yan Bindigar da ake zaton ‘yan kungiyar Asiri ne da akewa lakabi da Iceland cult group sun kai harin ne a jiya da safe a wani mataki da ake alakanta shi da na daukar fansa inda suka kashe Mutane 3.

'Yan kungiyar Asiri sun sheke Mutane 3 a jihar Rivers
'Yan kungiyar Asiri sun sheke Mutane 3 a jihar Rivers

Wata majiya dai ta bayyana cewa Mutane 3 da aka kashe basu san komai ba kuma ba ‘yan kungiyar Asiri ba, amma ana hasashen sun kashe su ne domin su razana Mutanen yankin ne kawai.

KU KARANTA: Allah daya gari bambam:Yadda wata kabila a Arewacin Najeriya ke ganawa da aljanu kafin su fara noma

Har dai ya zuwa lokacin hada wannan rahoto Kwamishinan ‘Yan sanda na jihar bai tabbatar da faruwar kai harin ba kuma majiyarmu ta gaza samun kakakin rundunar ‘Yan sandan jihar Nnamdi Omoni domin aji ta bakinsa.

Ana dai cigaba da samun karuwar kai hare-hare a yankuna daban-daban na kasarnan, wanda hakan ke jefa Mutane cikin zulli tare da fargaba. Sai dai ana jawabin shugaban kasa Muhammadu Buhari nay au da safe domin murnan Dimukuradiyya ya bayyana cewa, irin wadannan kashe-kashen da ake yin a mutukar bata masa kuma zasu yi duk mai yiwuwa a gwamnatance domin kawo karshensa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng