Hotuna da biyon yadda bakon haure ya ya ceci ran yaro dan shekara 4 a kasar Faransa
Wani bakon haure daga yammacin Nahiyar Afrika mai suna Mamoudou Gassama ya samu daukaka a idon duniya da ma kasar Faransa ta Nahiyar turai bayan da ya sadaukar da ran sa ya ceto ran wani yaro mai shekara hudu a duniya daga halaka a birnin Paris.
Kamar yadda muka samu, bakon hauren da ya fito daga kasar Mali an ce ya nuna matukar bajinta lokacin da ya hau wani bene mai hawa hudu domin ya ceto ran wani jariri da ya ga zai fado ta taga.
KU KARANTA: Wuta: Obasanjo ya fitar da rahoton binciken da EFCC tayi masa
Legit.ng ta ta samu cewa da yake ansa tambayoyin 'yan jarida bayan da ya ceto yaron, bakon hauren ya bayyana cewa ya sadaukar da ran sa ne saboda yaga shi yaro ne kuma yana bukatar taimako.
Tuni dai matashin bakon hauren mai shekaru ashirin da biyu a duniya ya samu alfarmar ganawa da shugaban kasar ta Faransa Emmanuel Macron wanda yayi alkawarin maida shi dan kasaa tare kuma da bashi aikin yi na din din din a kasar.
Haka ma dai a wani labarin kuma mun samu cewa tuni har mahukunta a kasar sun damke mahaifin yaron inda suka kai shi kotu bisa ga laifin barin yaron ba kula har ya kusa halaka kansa.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng