Duk mai rai mamaci ne: Yadda mamakon ruwan sama ya yi ajalin Alaramma, mahaddacin Qur'ani a garin Gombe

Duk mai rai mamaci ne: Yadda mamakon ruwan sama ya yi ajalin Alaramma, mahaddacin Qur'ani a garin Gombe

Wani labari dake da matukar kada zuciya da muke samu daga majiyar mu ta Rariya yana nuni ne da cewa ruwan sama da aka malala kamar da bakin kwarya a garin Gombe dake a shiyyar Arewa maso gabashin kasar nan yayi sanadiyyar ajalin wani Alaramma mai suna Bello Musa.

Kamar dai yadda muka samu, ruwan ya tafi da Alaramma Malam Bello Musa ne a cikin motar sa kirar Honda Civic a daren ranar Litinin din da ta gabata ne, bayan ya kammala jan sallar tarawihi a masallacin gidan Cikaire, kusa da fadar gidan gwamnatin jihar Gombe.

Duk mai rai mamaci ne: Yadda mamakon ruwan sama ya yi ajalin Alaramma, mahaddacin Qur'ani a garin Gombe
Duk mai rai mamaci ne: Yadda mamakon ruwan sama ya yi ajalin Alaramma, mahaddacin Qur'ani a garin Gombe

KU KARANTA: An gano ma'aikatan lafiya 6,000 na boge a jihar Sokoto

Legit.ng dai ta samu haka zalika cewa al'ummar unguwar dai sun ga motar Alaramman ne a cikin wani kwari tana ta kumbiya-kumbiya yayin da shi kuma yake a ciki yana ta neman agaji.

Sai dai bayan shafe lokaci mai tsawo na kusan sama da awanni uku ana ta kokarin fiddo Alaramman, ruwan wanda yake tafiya da karfin gaske a cikin kwarin ya kawo wa kokarin ceto shi cikas wanda daga baya dai aka fiddo gawar Alaramma din.

Allah ya jikan sa da rahama. Amin.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng