Ribar Ramadan: Gwamna Ganduje ya jagoranci musuluntar da mutane 90 a Kano

Ribar Ramadan: Gwamna Ganduje ya jagoranci musuluntar da mutane 90 a Kano

Kamar dai yadda labari yake iske mu cewa a yammacin ranar Litinin din da ta gabata ne dai mai girma Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci musuluntar da wasu magazuwa su kimanin 90 da suka hada da maza 38 da mata 52.

Su dai wadanda suka musuluntar kamar yadda muka samu daga majiyar mu ta Rariya, ance sun fito ne daga kananan hukumomin Sumaila, Garko da Takai dake a jihar kuma an ce sun karbi shahadar ne a masallacin gidan gwamnatin jihar ta Kano karkashin gidauniyar gwamnan ta 'Ganduje Foundation'.

Ribar Ramadan: Gwamna Ganduje ya jagoranci musuluntar da mutane 90 a Kano
Ribar Ramadan: Gwamna Ganduje ya jagoranci musuluntar da mutane 90 a Kano

KU KARANTA: Buhari mai gida na ne - Inji wani Gwamna a PDP

Legit.ng ta samu haka zalika cewa jim kadan bayan musuluntar ta su, Gwamna Ganduje ya kuma baiwa kowa daga cikin su Naira dubu 20 domin ya yi anfani da su wajen siyan kayan shan ruwa sannan kuma ya yi alkawarin bude musu makarantar addini a garuruwan su domin koyon ilimin addinin musulunci.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a makon da ya gabata ma Gidauniyar ta musuluntar da mutune 51.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng