'Yan Boko Haram 17 da suka mika wuya sun bayyana dalilin su

'Yan Boko Haram 17 da suka mika wuya sun bayyana dalilin su

Wasu daga cikin 'yan ta'addan kungiyar nan ta Boko Haram har su 17 da suka mika wuya ga dakarun jami'an tsaron Najeriya a kwanakin nan sun bayyana cewa dalilin da yasa suka mika wuya shine saboda sunji ance wai shugaba Muhammadu Buhari na ce zai yi masu afuwa.

Alhasan Ahmed da ke zaman daya daga cikin 'yan ta'addan da suka mika wuya ne dai ya shaidawa kwamandan rundunar sojin Najeriya din ta Operation Lafiya Dole dake yaki da 'yan Boko Haram din a garin Maiduguri Manjo Janar Rogers Nicholas hakan.

'Yan Boko Haram 17 da suka mika wuya sun bayyana dalilin su
'Yan Boko Haram 17 da suka mika wuya sun bayyana dalilin su

KU KARANTA: Dapchi: "Yan matan da aka sace watannin baya sun koma makaranta

Legit.ng ta samu haka zalika cewa 'yan ta'addan tun farko sun kuma bayyana cewa daman tun farko tilasta masu shiga kungiyar ta ta'addanci akayi kimanin shekaru hudu da suka shude.

A wani labarin kuma, Daya daga cikin barayin da suka fasa bankuna da dama a garin Offa, dake a jikin jihar Kwara dake zama daya daga cikin jahohin shiyyar Arewa ta tsakiya a Najeriya Michael Adiku ya sake fallasa wata katobarar da yayi.

Michael Adiku dai na zaman daya daga cikin jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya da ta kora kuma shugaban barayin da suka kai samame a bankunan a watanin baya wanda tuni ya ansa laifin sa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng