Ranar Yara ta Duniya: Daga yanzu duk mai abin hawan da ya kade yara zai shekara 2 a kurkuku

Ranar Yara ta Duniya: Daga yanzu duk mai abin hawan da ya kade yara zai shekara 2 a kurkuku

- A cigaba da shagulgulan bikin ranar Yara ta Duniya, Jami'an kare afkuwar haddura sun yi barazanar hukunci mai tsanani ga duk Direban da ya kade yara

- Shugaban hukumar na jihar Legas ne ya tabbatar da hakan a yau a wani bikin Yara da ya halarta

Hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) ta shaida cewa daga yanzu duk mai abin hawan da ya kade yara akan Titi zai iya fuskantar daurin shekaru biyu a gidan kurkuru.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa shugaban shiyyar hukumar mai kula da jihar Legas Mr John Meheux ne ya bayyana hakan yayin bikin ranar Yara ta Duniya na shekarar 2018 a yau Litinin.

Ranar Yara ta Duniya: Daga yanzu duk mai abin hawan da ya kade yara zai shekara 2 a kurkuku
Ranar Yara ta Duniya: Daga yanzu duk mai abin hawan da ya kade yara zai shekara 2 a kurkuku

Meheux ya bayyana damuwarsa kan yadda ake kara samun yawaitar kade kanann yara bisa tukin ganganci da direbobin suke yi, a saboda haka ne duk wani wanda jami’an suka kama zai fuskanci hukuncin shekaru biyu a garkame.

Sannan kuma duk direban da bashi da takardar izinin tuki amma suka cigaba da tuki har suka kade Mutane, to za’a tuume su ne aikata laifin kisan kai.

KU KARANTA: An damke wasu tsageru 3 da suka lalata Na’urar da take bawa gidan shugaba Buhari wutar lantarki

Kana kuma Meheux ya tabbatarwa Yaran cewa hukumar zata yi duk mai yiwuwa wajen kare lafiyarsu ba tare da abin hawa ya kade su ba yayin tafiya Makaranta ko wurin bauta.

Daga karshe ya kuma yi kira ga Yaran da su rika duba hanya sosai yayin da suke yunkurin tsallaka Titi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng