Hukumar kiyaye haddura ta fara daukar ma’aikata amma bisa sharadi guda

Hukumar kiyaye haddura ta fara daukar ma’aikata amma bisa sharadi guda

- Hukumar kiyaye haddura ta kasa (Road Safety) ta bayyana fara daukan mutane aiki kamar yadda Gwamnatin Tarraya ta bada izinin, ta bayyana hakan a shafinta na yanar gizo, inda ta ce duk wani mai sha'awar neman aikin zai iya ziyartar shafin nasu domin samun karin bayani

- Sai dai bisa sharadin duk wanda zai nemi aikin bai wuce shekaru 30 da haihuwa ba

Jami'in kula da harkokin da suka shafi ilimi na hukumar wato, Bisi Kazeem ya bayyana cewa akwai gurabe kamar Officer cadre, Marshal Inspectorate cadre da Road Marshal Assistant cadre su ne guraben da mai sha'awa zai iya cikewa.

Hukumar kiyaye haddura ta fara daukar ma’aikata a duk fadin Najeriya amma bisa sharadi guda
Hukumar kiyaye haddura ta fara daukar ma’aikata a duk fadin Najeriya amma bisa sharadi guda

Ya bayyana cewa su wadannan gurabe suna da wasu ka'idoji da aka shimfida musu domin cancantar cike su, gurbin Officer cadre ana sa ran wanda zai cike wannan gurbi ya kasance yana da shaidar karatun digiri na farko da kuma shaidar kamalla hidimar kasa wato (NYSC), sannan ya kasance bai wuce shekaru 30 da haihuwa ba.

KU KARANTA: Ma’aikatan kamfanin mai 28 sun makale, amma an ceto wasu 100 daga gobarar data tashi a kamfanin mai na Conoil

A daya gurbin kuwa na Marshal Inspectorate cadre, ya kasu har gida uku wato (MI-I, MI-II da kuma M-IIII), gurbin MI-I gurbi ne wanda ake bukatar mutum ya kasance yana da shaidar kamalla karatu na babbar difiloma ta kasa sai kuma shaidar kamalla hidimar kasa (NYSC), haka zalika kar ya wuce shekaru 30 na haihuwa.

Hukumar kiyaye haddura ta fara daukar ma’aikata amma bisa sharadi guda
Hukumar kiyaye haddura ta fara daukar ma’aikata amma bisa sharadi guda

Gurbin MI-II kuwa mutum ana bukatar ya kasance mai shaidar karatu ta bangaren da ya shafi harkar kiwon lafiya ko kuma ungozoma, kuma shekarunsa kar su wuce 28 na haihuwa.

Sai gurbi na karshe wato MI-III, shi ma shekarun neman wannan gurbi ana so kar su wuce 28. Sannan ya kasance mutum ne wanda yake da shaidar karatun ta babbar difiloma ta kasa a bangaren karatun da ya shafi cigaban muhalli.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng