Yanzu Yanzu: Shehu Sani ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar gwamna a jihar Kaduna
- Sanata Shehu Sani (APC, Kaduna) ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar gwamnan jihar Kaduna a shekarar 2019
- Sanatan ya bayyana kudirinsa na barin jam’iyyar APC, ya kuma bayyana cewa kwanakin Nasir El-Rufa’I a matsayin gwamnan jihar Kaduna kiirgaggu ne
- Sanatan yace zaben da aka gudanar a kananan hukumomi a ‘yan kwanakin da suka gabata an dauki sunayen wadanda akeso ne aka tura kawai, ba wai zabe akayi ba, wanda hakan yasa wadanda suka sayi form suka yi asara
Sanata Shehu Sani (APC, Kaduna) ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar gwamnan jihar Kaduna a shekarar 2019.
Sanatan ya bayyana kudirinsa na barin jam’iyyar APC, ya kuma bayyana cewa kwanakin Nasir El-Rufa’i a matsayin gwamnan jihar Kaduna kirgaggu ne.
Sanatan yace “zaben da aka gudanar a kananan hukumomi a ‘yan kwanakin da suka gabata an dauki sunayen wadanda akeso ne aka tura kawai ba wai zabe akayi ba, wanda hakan yasa wadanda suka sayi form sukayi asara tinda ba bari akayi kuri’a ta nuna ba.
“Saboda haka nake so gwamna El-Rufa’i ya sani cewa zan tsaya takarar gwamna 2019, kuma ba kananan hukumomi ne zasu gudanar da zaben ba, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), ita zata gudanar da wannan zabe, saboda haka kowane dan Najeriya zai kare kuri’arsa da kansa a bainar jama’a.”
KU KARANTA KUMA: Tompolo, Ateke Tom, tare da wasu shugabanni a Niger Delta sun nuna goyon baya ga gwamnatin tarayya
A baya Legit.ng ta rahoto cewa tsohon Shugaban Kasar Dr. Goodluck Jonathan ya karyata zargin sata inda yace sai da ya kammala ayyuka sama da 1000 a lokacin da yake rike da Kasar nan tsakanin 2010 zuwa 2015.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng