Jami’an sojin ruwa 2 da aka sace, sun tsallake rijiya da baya

Jami’an sojin ruwa 2 da aka sace, sun tsallake rijiya da baya

- Jami’an sojin ruwa 2 da aka sace a kan hanyar Jaji-Kaduna sun tsun tsallake rijiya da baya a hannun wadanda suka sace su

- Jami’an Lt-Commander S. Ahmed, wanda ke sashen makamai na wuta da kuma tukin jirgin ruwa (WEE/SBS), sai kuma Lt-Commander Maigado, matukin jirgi ta fannin harkokin jiragen sama na ruwa (AWW), aka sace a ranar Asabar da misalin karfe 10 na dare

- ‘Yan ta’addan sanye da kayan sojoji sun tare jami’an kilometre 2 daga Mararraban Jos, inda suka tafi dasu cikin daji

Jami’an sojin ruwa 2 da aka sace a kan hanyar Jaji-Kaduna sun tsun tsallake rijiya da baya a hannun wadanda suka sace su.

Jami’an Lt-Commander S. Ahmed, wanda ke sashen makamai na wuta da kuma tukin jirgin ruwa (WEE/SBS), sai kuma Lt-Commander Maigado, matukin jirgi ta fannin harkokin jiragen sama na ruwa (AWW), aka sace a ranar Asabar da misalin karfe 10 na dare.

‘Yan ta’addan sanye da kayan sojoji sun tare jami’an kilometre 2 daga Mararraban Jos, inda suka tafi dasu cikin daji.

KU KARANTA KUMA: Bikin ranar dimokradiyya ba shi da amfani a Najeriya - PDP

Bayan awowi hudu da suka yi suna tafiya suka tsaya domin tabbatar da babu jami’an tsaro dake biye dasu, sai daya daga cikin jami’an yayi kamar ya taka kaya, inda a kokarin ya cire ya shuri daya daga cikin ‘yan ta’addan a kai, sakamakon haka ne suka samu tsira, bayan sun ranci na kare suna kiran jama’a dasu taimaka masu.

Manya-manyan shugabannin kungiyoyin Nger Delta, sun daura damarar taya gwamnantin tarayya kokarin kara tabbatar da zaman lafiya a yankunan dake da mai domin samun samun gudanar da zaben 2019 cikin kwanciyar hankali.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng