Shirye-shiryen kayar da Buhari: An samar da Ofishin kamfen zaben Atiku na 2019
- Kura da fatar Akuya, Kungiyoyin dake goyon bayan Atiku sun shirya ganawar sirri a Dubai da Saudiyya da sunan Umrah
- Maganganu sunyi karfe kan cewa bayan Azumi za’a fara kamfe gadan-gadan
Bisa kusantowar zaben 2019 yanzu haka an fara girke murhun sanwar fara yakin neman zaben tsohon mataimakin tsohon shugaban kasa kuma Wazirin Adamawa Atiku Abubakar, domin kuwa maganar da ake har an samar da makeken Ofishin a garin Abuja da zai zama babbar shelkwatar kamfe na zaben 2019 .
Majiyar jaridar The Nation ta rawaito cewa, Ofishin mai hawa biyar da zai kasance shelkwatar kamfen an kama shi ne a Adetokunbo Ademola Crescent dake Wuse da Maitama a babban birnin tarayya Abuja.
Rahoton da majiyar mu ta rawaito ya nuna cewa yanzu haka magoya bayan Atikun na can kasar Dubai da Saudiyya suna gudanar da shirye-shiryen yadda zasu karbe kujerar mulkin kasar nan daga hannun APC.
KU KARANTA: Badakalar samar da wuta: Obasanjo ya fitar da sakamakon binciken da EFCC tayi masa
Domin da zarar an kammala Azumin zasu shiga shirye-shiryen kaddamar da yakin neman zabe.
Atiku dai na muradin uwar jam’iyyar PDP ta kasa ta tsayar da shi takarar zaben a 2019 bayan yayi fatali gami da ficewa daga jam’iyya mai mulki ta APC a watannin baya, wanda hakan wasu ke ganin na da wahalar yiwuwa duba da kasancewar akwai tsoffin ‘yan jam’iyyar da suke neman takarar.
Amma sai dai ko da aka tuntubi mai bawa Atikun shawara kan harkokin yada labarai Mr. Paul Ibe, cewa yayi bai ma san da maganar wancan makeken bene da ake magana ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng