Yan matan Dapchi da aka sace kwanan baya sun koma makarantar su ta da

Yan matan Dapchi da aka sace kwanan baya sun koma makarantar su ta da

Wani rahoto da gidan jaridar Muryar Amurka ya fitar ya nuna cewa wasu daga cikin 'yan matan makarantar kwanan nan ta garin Dapchi dake a jihar Yobe da 'yan ta'addan Boko Haram suka sace kimanin watanni 3 da suka shude sun koma makarantar.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a cikin watan Fabrerun da ya gabata ne 'yan ta'addan suka yi shigar burtu suka kwashe 'yan matan sama da dari sannan daga bisani bayan kimanin wata daya suka sako mafiya yawan su.

Yan matan Dapchi da aka sace kwanan baya sun koma makarantar su ta da
Yan matan Dapchi da aka sace kwanan baya sun koma makarantar su ta da

KU KARANTA: An gano ma'aikatan lafiya 6,000 na boge a wannan jihar ta Arewa

Legit.ng ta samu cewa wasu iyayen 'yan matan da suka maido yaran su makarantar sun bayyana cewa duk da suna tsoron a sake sace masu 'ya'ya, amma dai sun yanke shawarar cewa su maido su saboda ilimin na da muhimmanci sosai.

A wani labarin kuma, Biyo bayan wani aikin tantancewa da gwamnatin jihar Sokoto dake a shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya ta gudanar akan ma'aikatan lafiyar ta sama da dubu 13 gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal yace akalla dubu 6 an gano duk na boge ne.

Gwamnan dai ya bayyana hakan ne a yayin da yake kaddamar da wata cibiyar lafiya a matakin farko da kuma dakin ansar haihuwa a unguwar Gagi, dake a cikin birnin Sokoto.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng