Manyan ƴan wasa 4 da zasu iya barin Real Madrid ciki har da Ranaldo da Bale

Manyan ƴan wasa 4 da zasu iya barin Real Madrid ciki har da Ranaldo da Bale

- A jiya ne kungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta samu nasara akan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool da ci 3-1 a wasan ƙarshe na zakarun Zakarun Nahiyar Turai.A jiya ne kungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta samu nasara akan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool da ci 3-1 a wasan ƙarshe na zakarun Zakarun Nahiyar Turai.

Hakan dai ya bawa ƙungiyar damar kafa tarihin da ba a taɓa yi ba a gasar, sun kasance ƙungiya ta farko da ta lashe kofin har sau uku a jere.

Amma duk da wannan nasara da ta samu ana sa ran wasu manyan yan wasan kungiyar zasu iya sauya sheka zuwa wata kungiyar.

Ga jerin sunayen Ƴan wasa 4 da kuma dalilan da ka iya sawa su sauya sheka.

1- Gareth Bale

Manyan ƴan wasa 4 da zasu iya barin Real Madrid ciki har da Ranaldo da Bale
Manyan ƴan wasa 4 da zasu iya barin Real Madrid ciki har da Ranaldo da Bale

Wannan Ɗan wasa ya kasance ɗaya daga cikin manyan ƴan wasa a Zakarun Nahiyar Turai, sannan kuma jigo a kungiyar ta Real Madrid, amma sakamakon rauni da yake fama da shi a wannan kaka da kuma rashin katabus da yake yi a wasanni na baya-baya da aka buga yasa ya zama dan canji wanda baya daga cikin wadanda ake fara fitowa da su domin buga wasa.

KU KARANTA: UCL: Yadda Real Madrid ta lashe kofin Zakarun Turan ta na 13 a Tarihi

Hakan ya jawo hankalin wasu ƙungiyoyin suna zawarcin Ɗan wasan kamar ƙungiyar ƙwallon kafa ta Manchester United, Bayern Munich, Tottenham, PSG da sauransu.

Shi kansa dan wasan ya bayyana ra'ayinsa bayan da suka lashe kofin Zakarun Nahiyar Turai a jiya, ya bayyanawa manema labarai cewa "A gaskiya bana na samu kaina a tsaka mai wuya, amma zan zauna da wakilina domin tattauna makoma ta, naso ace nayi bajinta fiye da yadda nayi a yau amma rauni ya hana ni katabus"

2- Cristiano Ronaldo

Manyan ƴan wasa 4 da zasu iya barin Real Madrid ciki har da Ranaldo da Bale
Manyan ƴan wasa 4 da zasu iya barin Real Madrid ciki har da Ranaldo da Bale

Cece-kuce akan makomar Ronaldo ba wai sabon abu bane, an dade ana fama da hakan, tun kafin karshen wannan kakar wasannin ta bana rade-rade sun bayyana cewa ƙungiyar ƙwallon ta Manchester United tana sha'awar dawo da tsohon dan wasan nata, sai dai Kocin kungiyar Mourinho a kwanakin baya ya bayyana cewa hakan ba mai yiwuwa bane.

"Ronaldo babban dan wasa ne wanda ya kafa tarihi daban-daban a kwallon kafa, sai dai nasan abu ne mai wahalar gaske Madrid ta sayar da shi zuwa wata ƙungiyar musamman idan aka duba irin yadda ƙungiyar take samun nasara daga bangarensa." Inji Mourinho.

Amma a jiya bayan tattaunawar da manema labarai suka yi da shi jim kadan bayan kamalla wasan ƙarshe na Zakarun Nahiyar Zakarun Turai, Ronaldo ya bayyana cewa "Abun farin ciki ne da kuma murna ace na kasance daya daga cikin ƴan wasa da suka kafa tarihi a wannan ƙungiya." Sai dai wannan magana da ya yi yasa wasu na ganin cewar ko yana tunanin sauya sheƙan ne zuwa wata kungiyar.

3- Borja Mayoral

Mayoral ya kasance dan wasan gaba ne wanda ƙungiyar ta Real Madrid kai shi aro har sau biyu, amma daga baya ya dawo domin nuna bajintarsa sai dai Ɗan wasan har yanzu ya kasance a matsayin dan koran Karim Benzema, ma'ana cikon benci ne.

Shi ma Ɗan wasan a kwanakin baya ya bayyana ra'ayinsa cewa yana buƙatar ya sauya sheƙa domin yake samun damar buga wasanni akai-akai.

Yanzu dai haka Madrid tana kokarin karbo wani dan wasan nata daga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Levante domin ya maye gurbin Mayoral.

4- Dani Cebellos

Cebellos za a iya cewa yaro ne da ake sa ran nan gaba zai iya kasancewa ɗaya daga cikin taurari a kungiyar ta Real Madrid, sai dai ya fuskanci kalubale tun da ya baro ƙungiyarsa ta Real Betis zuwa Madrid.

Ɗan wasan ya samu kansa a matsayin dan canji wanda hakan ma baya samuwa sosai, dalili kuwa shi ne hakan ya samo asali ne bisa yawan ƴan wasan da ƙungiyar ke gare ta a gurbin da yake bugawa.

Sai dai rahotanni na nuni da cewa ƙungiyar zata iya bada shi aro domin ya samu gogewa zuwa wani lokaci. Daga cikin kungiyoyin dake zawarcinsa akwai Liverpool, Real Bestis, Valencia, Inter Milan da sauransu.

A yanzu haka dai ana jiran a kammala gasar cin kofin Duniya ne kafin kuma kowanne dan wasa yasan makomarsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng