Yan Bindiga sun kashe Mutane 30 a wani sabon hari a Zamfara
- Tsugunno bai kare ba kan batun matsalar kashe-kashen da ake yi a jihar Zamfara
- Harin baya-bayan nan yayi sandiyyar Mutuwar Mutane da yawa
- Sai dai kuma wannan karon yanayin kisan bayan ga tausayi ya zama abin takaici
Rahotannin da Legit.ng ta samu ya nuna cewa wasu ƴan bindiga sun bindige Mutane 30 har Lahira a jihar Zamfara.
Rahotannin da Legit.ng ta samu ya nuna cewa wasu ƴan bindiga sun bindige Mutane 30 har Lahira a jihar Zamfara. Rahotannin da Legit.ng ta samu ya nuna cewa wasu ƴan bindiga sun bindige Mutane 30 har Lahira a jihar Zamfara.
Rahotan ya bayyana cewa ƴan bindigar sun kai harin ne a ƙauyen Malikawa dake Gidan Goga a ƙaramar hukumar Maradun ta jihar.
Bayan kai harin ƴan bindigar sun kashe wasu Mutane biyar ne da suka je Gonakinsu Noma sanna yayinda Mutane suka isa inda gawarwakin waɗanda aka kashe suke domin yi musu jana'iza, sai suka buɗe musu wuta suka riƙa harbi kan mai uwa da wabi wanda hakan yayi sanadiyyar Mutuwar ƙarin wasu Mutanen har 25.
KU KARANTA: Nau'ikan Abincin da ya kamata a gujewa ci da safe, na 5 zai baka mamaki
"Da sanyin safiya ne ƴan bindigar dake da maɓaya a dajin suka kashe Manoman yayinda suka je domin aikin Gona." Kamar yadda wani mazaunin yankin main suna Mallam Makau ya bayyana
"Kuma ganin Mutane sunje domin ɗauko gawarsu ayi musu jana'iza ne suka rinƙa harbi har suka kase 25 daga cikinsu."
Kakakin rundunar Ƴan sanda na nihar Muhammad Shehu, ya tabbatar da faruwar lamarin sai dai ya alaƙanta shi da rikici kan filaye tsakanin ɓagarorin biyu.
Sannan ya shaida cewa yanzu haka an tura jami'an domin saisaita al'amura a yankin.
Biyo bayan wannan sabon harin da aka kai, adadin waɗanda suka rasa rayukansu ta sanadiyyar irin wannan rikici yanzu yakai har Mugane 189 daga watan Fabarairu zuwa yanzu a jihar ta Zamfara.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng